Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Asabar cewa, yayin da duniya a yanzu ke cikin wani muhimmin yanayi, ya kamata Sin da Faransa su hada hannu wajen bude hanyar samar da zaman lafiya da tsaro da wadata da ci gaba domin kyautata rayuwar bil Adama.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne yayin da suke taya juna murna da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, kan cikar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashensu shekaru 60 da kulluwa.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Zai Tattauna Da Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Tsaro Yayin Ziyararsa A Thailand
- Amurka Na Daukar Barazanar Da Sin Ke Kawowa A Matsayin Dalilin Fadada Karfin Sojanta A Sararin Samaniya
Xi Jinping ya kara da cewa, cikin shekaru 60 da suka gabata, kasashen biyu sun rungumi muhimman zabuka da kansu ba tare katsalandan daga bangarorin waje ba, haka kuma sun kasance masu neman ci gaba na bai daya ta hanyar hadin gwiwar moriyar juna da inganta koyi da juna ta hanyar musaya tsakanin al’ummominsu da hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya karkashin hadin gwiwar bangarori daban daban.
Har ila yau, ya ce yayin da ake fuskantar sauye-sauye da tarihi game da inda ya kamata duniya ta dosa, a matsayinsu na manyan kasashe kuma mambobin dindindin a Kwamitin Sulhu na MDD, ya kamata Sin da Faransa su tsaya ga ainihin burinsu na kulla dangantakar diplomasiyya da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare da bude hanyar samar da zaman lafiya da tsaro da wadata da ci gaba, domin kyautata rayuwar bil Adama. (Fa’iza Mustapha)