Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da hada karfi da karfe wajen gina kyakkyawar kasar Sin, da kuma sa kasar ta kara zama kore shar ta hanyar dasa itatuwa.
Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar aikin sa kai na dashen itatuwa a nan birnin Beijing a yau Alhamis. Yana mai cewa, a halin yanzu, yawan gandun daji na kasar Sin ya zarce kashi 25 bisa dari, wanda ya ba da gudummawar kusan kashi 25 cikin dari na sabon koren yanki na duniya. Kana yanayin muhalli yana ci gaba da ingantuwa, kuma mutane na ganin hakan a zahiri. A sa’i daya kuma, ya kamata a lura cewa, har yanzu akwai karancin gandun daji da ciyayi a kasar Sin, kuma ingancinsu da kyansu ba su wadatar ba. Ya kamata a magance matsalolin da ke kasa, kuma a yi kokarin kara kyautatawa kowace shekara. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp