Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da sabon zababben shugaban kasar Liberia Joseph Nyumah Boakai, ta yadda sassan biyu za su zurfafa kawance da amincewa da juna, da karfafa hadin gwiwar cimma moriya tare.
Xi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, cikin sakon taya murnar lashe zabe da ya aikewa shugaba Boakai. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp