Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron karawa juna sani a Alhamis din nan, inda ya yi kira da a kara zurfafa sauye sauye masu nasaba da zamanantarwa irin ta Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwa ta rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne yayin da ya jagoranci taron a birnin Jinan dake lardin Shandong, wanda ya samu halartar wakilai daga sassan ‘yan kasuwa da masana daga jami’o’i. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp