Falasɗinawa da suka koma Gaza bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas sun fara bincike a baraguzan gine-ginen da aka rushe domin neman ‘yan uwansu da suka ɓata.
Mahmoud Basal, mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta Falasɗinawa, ya ce suna neman mutane kusan 10,000 da suka rasa rayukansu a ƙarƙashin gine-gine sakamakon hare-haren bama-baman da suka lalata gidajensu.
- Trump Ya Sake Ɗarewa Kan Mulkin Amurka, Sabbin Ƙudirorinsa Sun Bar Baya Da Ƙura
- Sin Ta Yi Maraba Da Matsayin Da Najeriya Ta Samu Na Zama Abokiyar Huldar Gamayyar BRICS
Ya ƙara da cewa gawarwaki aƙalla 2,840 sun narke ba tare da alamunsu ba.
Rahotanni daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da kashi 90 na gidajen Gaza sun rushe, yayin da sharar gidajen da suka lalace ta kai tan 50.
An ƙiyasta cewa za a ɗauki shekaru 21 kafin a kwashe sharar gaba ɗaya, wanda zai ci kuɗi har Dala biliyan 1.2.
Wani rahoton ya bayyana cewa sai shekarar 2040 za a iya sake gina Gaza, yayin da rahotanni suka ce yakin ya jawo Gaza ta koma matsayin ci gaban da ta ke da shi shekaru 69 da suka gabata.
Isra’ila ta bayyana cewa manufar hare-haren da ta kai shi ne murƙushe ƙungiyar Hamas gaba ɗaya da lalata dukkanin hanyoyin da ta ke amfani da su a ƙarƙashin ƙasa.