Ya Kamata A Jinjina Wa Wadanda Suke Gudanar Da Zabukan Shugabannin APC – Inuwa Yahaya

 

Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, yana cikin ‘yan takarar gwamna karkashin tutar jam’iyyar APC a Jihar Gombe, a wannan tattaunawa da yayi da LEADERSHIP A YAU Asabar, ya tsokaci batun zaben shugabannin APC da aka gudanar a mazabu makon da ya gabata, da kuma zabukan shugabannin jam’iyya a matakan kananan hukumomi a yau. Ga yadda ta kaya.

APC ta gudanar da zaben Gundumomi a jihar Gombe, sai dai wasu suna cewa ba a yi zaben ba; wasu kuma suna cewa an yi mene ne za ka fada wa jama’a ganin cewar kana cikin jiga-jigai a jam’iyyar nan?

To, ni a tawa fahimtar an yi zabe, daman tsarin zabe da yadda za a gudanar da zaben shi ne yake sanyawa a san an yi ko ba a yi zaben ba, ta yadda aka taho daga tsarin uwar jam’iyyar ta kasa, kwamitin da aka nado wanda ya zo da tsarin jadawalin yadda ya kamata a gudanar da zabe, kuma aka yi zaben a bisa tsarin. Tsarin kashi biyu ne, walau jama’an da suke Gunduma su yi ittifakin cewa shugabaninsu da suke kai a halin yanzu su ci gaba a bisa dalilai na kaza da kaza. Idan aka je wajen yin zabe sai su amince, su ce eh mun amince, ka ga sai su zarce. Inda kuma aka samu kan-kan-kan, wani ya ce yana so har ma ya sayi fom ka ga ya nuna sha’awarsa aka kuma gagara cimma matsaya sai a je a buga kuri’a ta raba. An yi dukkanin wannan kashi biyu, kuma dukka a nan Gombe, kuma wani ya zo ya ce ba a yi zabe ba?. Ni kam a guna an yi zabe kuma zabe mai inganci na gaskiya da adalci cikin nagarta.

Mun yi zama na musamman na masu ruwa da tsaki a cikin wannan jam’iyyar a kwanakin baya da suka wuce, kuma a wannan zaman mun zauna mun duba muka ga yadda muka taho, da iya abun da aka samu na kuri’un nan da kuma gudunmawar da wadannan shugabanin suka yi wajen ganin mun kai ga samun nasarori a zaben shugaban kasa, Sanataci har ma na gwamnan ma da ake kayin magana a kai, wadannan sune suka taka rawa har aka samu wannan nasarar, don haka basu kawo wani nakasun da zai sanya a ce a cire su ko a canza su ba, illa dai mu tace kai mu tsefe wadanda suka cutar da mu, mu cire baragurbi, mu kawo wadanda suke sabbin jini mu hada sai su yi gwagwarmayar yadda za mu kai ga samun nasarar kafa gwamnati a jihar Gombe, da ma sauran dukkanin kujeran zabukan da za a yi a Nijeriya.

Akwai ‘yar tirka-tirka da aka samu da shugaban kwamitin gudanar da zabe, amma daga baya dai ya ce a je dai a yi zaben, mene ne kake tunanin jama’a suke ta wannan korafin?

Ai ni misalin da zan maka ita kanta hukumar zabe wacce take da alhalin shirya zabe a kasar nan, idan ta tashi shirya zabe ba fa a dare daya rana daya take shiryawa ba, yakan dauki watanni. Yanzu zaben da za a yi na 2019 ina tabbatar maka a yanzu har ta bayar da sanarwar cewar za a yi a watan kaza tun watannin baya. Ita kuma wannan jam’iyyar an zo a cikin yanayi na matsi a cikin kuma karancin lokaci, aka ce za a yi zaben nan. idan ka kwanta a gidanka kana tsammanin cewa abu zai zo ya iskeka wannan sai ka samu matsala, amma idan kana bin jam’iyya, kuma kana tafiya a kai za ka san yanda za a yi zabe kuma da cewar za a yi, kuma aka zo aka yi zaben, wannan shine. Da kaman ma ai cewa aka yi jagororin su zarce, aka duba aka ce a je dai a yi wannan zaben, to lokaci na kurancewa, kuma ana son a samu lokacin da za mu daidaita kawukanmu domin mu samu yadda za mu tafi har mu kai ga zaben 2019 da ke tafe. Don haka bai zamanto akwai lokaci wadatacce ba, a guje aka kafa kwamiti, a guje kwamiti ya zo aka shiryo kuma kwamitin daukaka kara in an samu akasi ko wani kuskure wanda ya ja kuma ya ga zai kai kokensa wajen kwamitin domin su duba shi ma zai iya kaiwa, saboda haka dukkan matakan da suka dace a yi zaben nan sahihi kuma da inganci an yi shi, sannan kuma za a ci gaba da yin dukkanin abun da ya dace domin ita jam’iyyarmu ci gaba ne a gabanta.

Yau ake gudanar da zaben shugabannin APC a matakin Kananan hukumomi na APC, wane tabbaci ne za ka bai wa jama’a ganin cewar ‘yan kurakuran da aka samu a na Gundumomi an gyara su?

Tabbacin da zan bayar a bisa matakan da na ga uwar jam’iyya ta dauka ne, an kafa kwamitin yin zabe, an turo mana mutanen da suka san kan zabe, kuma gogangu ne a hidimar siyasa suka iya siyasa, kamar misali wanda ya zo nan ya jagoranci zaben Gundumomi Honorabul Kawu Sumaila,kowa ya san shi ya kuma san gwargwamarsa a siyasa, wanda ya yi masa Sakatare Umar Kareto kowa ya san shi ya san matsayinsa a siyasa, da sauran kwamitocin mutane bakwai wadanda dukkaninsu gwanaye ne a hidimar siyasa, wadanda da sune aka yi tsari a uwar jam’iyya kuma aka turo su, wadannan mutanen za su iya cire mana kitse a wuta, kuma masu kokarin kawo daidaito ne, domin haka ina kira ga ‘ya’yan jam’iyya su zauna kan tsarin jam’iyya su zauna bisa hurumin doka da kuma tsarin da aka baiwa wadannan mutanen domin mu samu mu fita tare mu tsira tare gaba daya.

Kusan su wadanda suka nuna tawaye masu nuna cewar ba yi musu daidai ba, shi za ku wofintar da su ne ko kuma za ku sake dawo da su domin ku nuna musu hanyar da suka dauka ba daidai ba ne su zo a gyara?

Ina son na yi amfani da wannan damar na yi kira ga sauran ‘ya’yan jam’iyya da cewar su gane yanayin da muke ciki musamman a jihar Gombe. Jam’iyyar nan fa akwai wadanda aka yi mana cushe aka shigo mana da su suna neman su dada farraka mu, su daidaita mu domin kada mu samu hanyar kaiwa ga nasara; daman can baya irin wannan matsalar aka samu, wasu aka saye su, suka shiga suka farraka jam’iyya suka saida mu suka yi gaba. Yanzu idan muka sake budewa, to, Allah ya sauwaka. Amma ina kira ga ‘ya’yan jam’iyya su tsaya su gane cewar fa su wanke idanunsu su gane cewar su waye wadannan mutane domin su yi maganinsu, yanzu abun da ke ganamu ci ne mu fuskacin kalubalen da suke gabanmu musamman wadanda aka shigo mana da su cikin jam’iyya.

Ina maganar sake neman gwamna ne, ganin cewa ka nema a baya Allah bai baka ba, me kuma za ka ce wa magoya baya da jama’an Gome?

Abun da zan ce ga masoya da magoya baya na, shi ne Muhammad Inuwa Yahaya yana nan kuma da yardar Allah ina cikin takara, kuma zan tsaya takara, kuma cikin yardar Allah zai kai ga nasara a wannan karon, domin an sha mu mun warke mun san hanyar da za mu bi, kuma in Allah ya yarda za mu yi mulki a jihar Gombe, masoyanmu su san da wannan ina shirye kuma na fito neman gwamna a 2019 a jihata ta Gombe.

Wane yunkuri za ku yi a APC wajen ganin kun amince, kun fitar da masu neman gwamnan nan daidai kima, domin a 2015 kusan ku 3 ne kuka fito, yanzu kuma ga ‘yan takarkaru da yawan gaske?

A wannan yanayin jam’iyya ita ce da kuma shugabanin na jam’iyya sune ya kamata su jagoranci dukkanin ‘yan takarkaru da dukkanin ‘ya’yan jam’iyya bisa tsarin na tafiyar jam’iyya ba, bisa tsari na tafiyar biyan bukatar wasu kalilan ba. A tsaya a duba bisa tsari a yi tunani a yi kara, ba kawai don ka yi takara da mutum shi kenan ya zama abokin gabarka bane, a’a, abokin takara ne, abokin fahimta ne, abokin mujadala ne ta yadda za yi a tattauna domin a samu maslaha da sulhu a yanayin da muke ciki, idan aka yi abun da ya dace, ba yawan dan takara shi ne damuwar ba, amma rashin adalci da rashin kyautatawa shine zai kai ga rashin kawo wa dan takara ci gaba da jama’a hade da kasa. Kuma shi fa shugaba makiyayi ne, Allah kuma ya yi alkawarin zai tambayi kowa bisa abun kiwon da ya bashi. Don haka idan ka amince ka shiga aka cutar da jam’iyya, aka cutar da jama’a ka tabbatar da cewar akwai makoma, kuma ina tunanin wadanan mutanen sun koyi darasi domin a abubuwan da wasu suka yi a baya, wanda har ta kai an cire wasu daga jam’iyar nan, kuma ni a ganina a shugabancin jam’iyya a jihar Gombe a wasu wuraren akwai gyara, a wasu wuraren kuma babu gyara. Ka sani wasu jagoririn APC a jihar nan sun takara rawa sosai barin su ci gaba da mulki shine mafi a’ala, domin ku sani a zaben 2015 sune suka yi kokari har aka samu kashi 85 na zaben shugaban kasa duk da cewar PDP ce ke mulki a jihar, aka ci sanatoci biyu a cikin uku, aka ci wakilai hudu a cikin shida, muka ci majalisar jihar guda 10, aka yi zaben gwamna ni da gwamna mai ci da kadan ya fini a kuri’u, wadannan jagororin jam’iyyar sune suka kawo wannan nasarar, a duba a ga ina ne da matsala a gyara, wadanda basu da matsala a hade a yi tafiya wajen guda domin babu wata matsala ta kwace mulki daga PDP a jihar nan.

Wane tabbaci ne za ka bayar na cewar a cikinku masu neman takarar nan idan dayanku ya samu zai yi adalci ga sauran?

Mu ai ba ma wa mu ba, wa magoya bayanmu ma sun hadu sun hade kansu sun yi zama kashi-kashi kuma har yanzu ana kan wannan zaman, APC a dinke take a Gombe, domin daman Baba Buhari ya fada mana cewar jiki magayi, to jikinmu ya gaya mana, yanzu mun hadu mun hade kuma za mu kai ga samun nasara cikin yarda Allah a tsakaninmu.

 

 

Exit mobile version