Gamayyar kungiyoyin matasan arewa mazauna Legas sun bayyana cewa lallai Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya saurari koke-koken al’ummar kasar nan wajen kara yawan adadin kudaden da za a dunga cirewa a duk kullum.
A baya dai, CBN ya kakaba dokar kayyade cire kudade wanda a duk kulum mutum zai iya cire naira 20,000, yayin da a mako mutum zai iya cire naira 100,000 kacal.
- Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- NIS Ta Bankado Sabbin Dabarun Da Masu Safarar Mutane Ke Amfani Da Su A Jihar Bayelsa
Sai dai daga baya CBN ya kara yawan kudaden ya tashi daga naira 100,000 zuwa naira 500,000 a duk mako. Inda kamfanoni za su iya cire naira miliyan 5 maimakon dubu dari biyar a mako. Dokar kayyade kudaden za ta fara aiki ne tun daga ranar 9 ga watan Janairun 2023.
Mafi yawancin al’ummar Nijeriya sun nuna gamsuwarsu game da wannan mataki da CBN ya dauka na kara yawan kudaden, wanda suke ganin cewa lallai CBN ya saurari koke-koken al’ummar kasar nan.
Shugaban gamayyar, Alhaji Ibrahim Galadanci ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce, “A matsayina na wadanda muke mu’amala da al’umma muna ganin sauya wannan salo da CBN ya sauya ya ji kiran talakawa. Ma’ana gwamnati ta sausauta wa marasa karfi.
“Dama mu abin da muke hange a nan shi ne, salon da CBN ya dauka kan wannan dokar kayyade kudade, ya faru ne sakamakon bata-garin ‘yan siyasa da suke wadaka da kudaden al’umma. An kakaba wannan doka ne saboda a taimaka wa al’umma, domin akwai wadanda suke sana’a a bangaren harkokin kudi da suka yi rajista da POS.
“Kamar mutumin karkara wanda ba lallai ba ne sai ya je banki. Zai iya sayar da amfanin gonarsa ya samu mai POS ya ba shi ‘yar dubu darinsa ya saka masa a asusun bankinsa.
“Tsarin da gwamnati ta bullo da shi a wannan karan, mu dai a bangarenmu gwamnati ba ta taba yin wani abu wanda muka ji dadinsa sama da wannan ba. Domin gwamnati ta fito da doka kuma ‘yan kasa suka fito suka yi ta korafi a kan gwamnati ta sassauta kuma har ta saurari koke-koken al’umma,” in ji Ibrahim Galadanci.