Daga Abba Ibrahim Wada
Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, Kojo Williams ya ce, akwai buƙatar tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta ƙasa su kai wasan kusa da na kusa da ƙarshe (Ƙuarter Final) saboda suna da ‘yan wasan da za su iya zuwa wannan matsayin.
Williams ya ce, yanayin yadda ‘yan wasan suke buga wasa a yanzu da yadda suka buga wasannin neman cancanta, tabbas suna da ƙwarewar da za su iya taɓuka wani abu, gasar da za a gudanar a ƙasar Rasha.
Ya ci gaba da cewa, “yawancin ‘yan wasan sababbi ne kuma masu jini a jika, saboda haka ‘yan wasan suna buƙatar goyon baya daga hukumomi domin ganin ƙasar ta yui abin arziƙi a ƙasar Rasha.