Kasar Sin ta kasance abin misali a duniya wajen samun ci gaba, kamata ya yi kasar Senegal ta dauki kasar Sin a matsayin abin koyi da zaburarwa.
Babban darektan gidan yada labarai na kasar Senegal Sambou Biagui ne ya bayyana hakan a cikin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya, yana mai cewa, kasar Sin ita ce kasa mafi dacewa da Senegal za ta yi koyi da ita, don tana samar da damammakin yin hadin gwiwa.
- Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Kawo Moriya Ga Bunkasar Masar
- Xi Ya Yi Kira Da A Gudanar Da Aikin Tantance Harkar Kudade Mai Inganci Don Inganta Bunkasar Tattalin Arziki Da Zamantakewa
Biagui ya kara da cewa, hadin gwiwar da kasar Sin ta gabatar ta dogara ne kan mutunta juna, wanda ya bayyana dalilin da ya sa kasar Sin ke ba da shawarar yin hadin gwiwa da samun nasara tare.
Ya ce, farawa da aikin gona, a halin yanzu kasar Sin ita ce kasa mafi dacewa da Senegal za ta iya yin koyi da ita, yana mai jaddada bukatar kasar Senegal ta hada kai da kasar Sin don yin amfani da wannan dama da kuma samun ci gaba na hakika.
Biagui ya kara da cewa, kamata ya yi Senegal ta yi amfani da wadannan fannonin da aka tabbatar da yin hadin gwiwa da kasar Sin, ta bunkasa ayyukan samar da yadi da auduga, yayin da take samarwa da sarrafa gyada, da mai da iskar gas a cikin gida. (Mohammed Yahaya)