A yayin da ake ci gaba da neman shugaban jam’iyyar All Progressibes Congress (APC) na kasa, Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya yi kira ga Jam’iyyar APC ta kasar da ta yi adalci ga rushasiyar jam’iyyar Congress for Progressibe Change (CPC) da jihar Nasarawa.
Injiniya Sule ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan da ya sake tabbatar da katin zama dan jam’iyyar ta APC, a mazabarsa ta Gudi Motor Park II, da ke garin Gudi a Karamar hukumar Akwanga, a ranar Talata.
Da yake bin diddigin tarihin kafuwar CPC a Jihar Nasarawa, Gwamnan ya nuna cewa idan Najeriya za ta yi wa CPC adalci to Jihar Nasarawa ita ce wurin da za a duba.
Injiniya Sule ya yaba wa magabacinsa na yanzu, Sanata Umaru Tanko Al-makura, kan yadda ya kawo wa jam’iyyar ta CPC martaba, inda jam’iyyar ke da jihar Nasarawa kawai a matsayin yarjejeniyar ciniki a lokacin hadaka da ta kawo APC.
A dalilin haka ne Gwamnan ya ce ya yi imanin cewa, ta kowace hanya ce, idan Najeriya za ta kyautata wa CPC, to ya kamata kasar ta tausaya wa Jihar Nasarawa.
Gwamnan ya sake kira ga jami’an da ke gudanar da aikin sabunta ridistan kada su nuna wariya a bakin aikin su suba kowa damar yin rajista.
Da yake jawabi a wurin taron, Sanata Al-makura ya ce taron mutane da suka yi hargitsin wadanda suka halarci taron, ba wai kawai suna nuna irin goyon bayan da jam’iyyar ke samu ba ne har da nuna kauna ga Jam’iyyar APC.
“Sabunta katin yana da muhimmanci. Dole ne dukkanmu mu fita don tabbatar da nasarar jam’iyyar,” in ji Sanata Al-makura.
Shi ma Sanata Abdullah Adamu ya yaba wa Gwamnan kan yadda yake tafiyar da kowa a cikin Gwamnatin sa da kuma yadda yake gudanar da kyawawar ayyukan cigaban a Jihar Nasarawa.
Ya kara da cewa fitowar mutane a wurin taron, ya kasance shaida cewa APC ta kasance jam’iyyar da za ta doke duk wata Jam’iyyar adawa a jihar, idan akwai.
Tun da farko, Shugaban Kwamitin riko na Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa Hon. John Mamman, ya bukaci ya’yan jam’iyyar da kaucewa karya ka’idoji da dokokin gudanar da aikin sake tantancewa da rajistar.