Tambaya:
Assalamu Alaikum. Da fatan Malam ya na lafiya. Malam don Allah ina da tambaya; Mutum ne ya musulunta, bayan ya karbi musulunci ya kira matansa a waya suma suka musulunta kafin yadawo sai ya rasu. Matan Kuma su bakwai ne. Yaya za ayi wajen rabon gado?
Amsa:
Wa’alaikumus Salam Wa Rahmatullah. Toh dan uwa Lallai ya wajaba a gare su dukkansu su yı idda, Sannan Za su yı sulhu a tsakaninsu su barwa mata hudu su ci gado, in kuma suka ki yin sulhu sai ayi Kuri’a a tsakaninsu, a zabi guda hudu ta hanyar Kuri’a, a basu gado.
Allah ne mafi sani.
Ana Bi Na Ramakon Azumi, Amma Ina Kokonton Yawansu, Yaya zan Yi?
Tambaya:
Assalamu alaikum Mal Mace ce Tasha Rabin axumi kuma bayan axumin Ya wuce ta ranka Sai dai ba duka ba yanxu Tana so ta ida Amma ta manta axumin Nawa tayi baya Tana ganin batayi Rabi ba kuma Tana ganin kamar tayi rabi Amma ita ta manta DAN ALLAH MAL YA XATAYI??
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta yi gini ne akan tabbas wajan ramako, misali idan kına zaton ashirin suka rage miki ko kuma ashirin da biyar, to sai ki rama ashirin da biyar (25), saboda in kin yi haka za ki fita daga kokwanto, kuma zai zama tabbas kin rama abin da ake binki.
Allah ne mafi sani.
Tambaya:
Assalamu Alaikum dafatan katashi lfy, Allah yakara basira. Don Allah ina so a amsa mini wannan tambayan ko abamu shawara, ina da abokina/amini na mun tashi tare mun yi karatu tun daga matakin primary har zuwa jami’a tare muka gama, mun zama kamar yan uwa. Abokina yayi aure wata hudu da suka wuce kuma daga baya yake samun labarin matar tashi bata kama kantaba kafin ya aureta, Harma ya hadu da wassu daga cikin wadda suka sadu da ita kafin ya aureta, kasancewa ba a gari daya suke ba a makaranta suka hadu, kuma yayi iya binciken halinta kafin ya aureta amma bai gano rashin kamun kantaba.
Kuma a halin yanxu yace ta fita a ransa tun da yaji labarin abubuwan da tayi a baya, A matsayina na amininsa nace kar yayi hukuncin da babu shi a sharia da sunnah ya bari mutura tambaya a malamanmu na sunnah domin samun cikekkan amsa da shawarwari . Nagode
Amsa:
Wa’alaikum assalam, Mutukar ta tuba, kuma ingantaccen tuba ne, zai iya cigaba da zama da ita, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba aikatawa ne ba.
Sai dai in har ya daina sonta kwata kwata, to rabuwa ita ce mafita, saboda duk matar da ba ka so, to za ba ka iya tsayawa da hakkokinta ba.
Rayuwar aure tana ginuwa ne akan soyayya da sha’awa, idan daya ya samu tangarda, aure ba zai tafi a SAITI ba.
Allah ya shar’anta saki ne saboda tunkude cuta daga ma’aurata ko kuma daya daga cikinsu.
Ina baka shawara da ka kara bincike da nazari saboda Makiya da Mahassada da Magauta suna iya bata mutum da tsagwaron Kage.
Allah ne mafi sani.
Ana Yin Wa’azi Ne A Inda Wa’azin Zai Yi Amfani !
Amma in za’a samu sabani, ka tsaya a wa’azi shi ne wajibin ka, saboda fadin Annabi (SAW) “Wanda ya ga mummuna a cikinku to ya canza shi da hannunsa, in ba zai iya ba ya canza shi da harshensa (ta hanyar wa’azi), in ba shi da dama to ya ki abin abin a zuciyarsa”.
A cikin Suratu A’alah, Allah ya yi bayani cewa: Ana yin wa’azi ne, idan wa’azi zai yi amfani.
Allah ne mafi sani.
Ba Na So Na Sha Azumi, Ko Zan Iya Shan Maganin Hana Haila ?
Allah ne mafi sani.
Akwai Zakka A Cikin Hajar Kasuwanci!
Tambaya:
Assalamu alaikum. Malam, Na karbi loan a Ja’iz Bank shekaru uku da suka wuce, na kuma shiga harkar gina gidaje, a yanzu na gama biyan kudin a January 2020. Gidajen da na gina a Millinion City 2 & 3 bedroom flats ne, amma fa suna kasuwa.
1.Tambaya ta ita ce, shin akwai Zakkah a cikin wannan, idan akwai, yaushe ya kamata a fitar?
Saboda a yanzu shekara daya kenan gidajen na kasuwa ba’a riga an sayar ba.
- Tambaya ta biyu.
Mai dakina tana sana’ar kayan Kitchen yau shekara Ukku, Kuma Allah yasa Albarka a cikin sana’ar, yaushe ya kamata ta fidda Zakkah? saboda, wasu kudin suna hannun mutane a matsayin bashi, wasu hajane watau (kayan kitchen) ba’a riga an sayar ba.
Sannan akwai kudi a banki, amma basu isa Zakkah ba.
Shin Yaya za’a fitar da Zakkah a wannan halin? saboda idan aka hada kudin dake banki, da hajar dake kasa da kudaden dake hannun mutane na bashi, kudin sun kai Nisabin Zakkah.
Na gode, Allah Ya saka da Alheri, amin.
Amsa:
Wa alaikum assalam. Gidajan da aka yi don siye da siyarwa ana fitar musu da Zakka in sun Shekara kuma sun kai nisabi, saboda sun zama kayan Kasuwanci, kayan Kasuwanci kuma ana fitar musu da Zakka kamar yadda Ibnu Abi-zaid Alkairawany ya yi bayani a Risala shafi na (66).
Mutumin da yake Kasuwanci, ya wajaba duk Shekara ya kaddara hajarsa da kuma kudin da suke hannunsa da kuma na banki, mutukar jumalarsu sun kai Nisabi kuma sun Shekara, zai fitar da Zakka.
Ana kasa jumlarsu ne gida Arba’in, sai a bada kashi guda.
Allah ne Mafi sani.
Me Ya Sa Aka Bambanta Namiji Da Mace A Wajan Rabon Gado?
Tambaya:
Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?
Amsa:
Wa’alaikum assalam, Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin haka, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar.
Allah da kansa ya raba gado bai wakilta wani don ya raba ba, ya bawa kowa hakkinsa gwargwadon kusancinsa da mamaci da kuma masalahar da Allah ya duba, wacce ya fi kowa saninta.
Daga cikin hikimomin da suka sanya shariar Musulunci ta bambanta tsakanin mace da namiji a rabon gado shi ne: kasancewar hidimar namiji ta fi ta mace, yawancin mace idan tana karama tana karkashin kulawar mahaifinta, idan kuma ta yi aure tana komawa cikin kulawar mijinta.
Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya sabawa ayoyin rabon gado a cikin suratun Nisa’i aya:14, kamar yadda ya yi alkawarin Aljanna mai koramu ga wanda ya bi rabon da ya yi a cikin aya ta:13 a waccar Surat.
Duk Wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya sabawa Allah, to yana nan a madakata, kuma mabuwayi ne mai tsananin karfi kamar yadda ayoyin Alkur’ani masu yawa suka tabbatar.
Allah ne mafi sani.
Fatawar Rabon Gado (170)
Tambaya:
Assalamu Alaikum Malam dafatan alkhairi Allah yakara lafiya Amin. Macece ta mutu bata taba haihuwa ba. Ba ta da kowa sai ‘ya’yanta kuma shi ma ya rasu amma ya bar ‘ya’yansa maza da mata. Malam ya za a raba gadonta, Wassalam.
Amsa:
Wa alaikum assalam
Za’a bawa ‘ya’yan yayanta maza kawai ban da mata.
Allah ne mafi sani