Gidan aure gida ne na zama har abada, zama ne da aka faro shi a sanadin soyayya. Zaman gidan aure zama ne da ke bukatar nuna kulawa ba da lokaci da kuma sadaukarwa.
Duk wadannan abubuwan suna samuwa ne ta hanyar hadin kai da uwargida da kuma shi kanshi Mijin. Zaman aure zama ne da ke bukatar lokaci, to in akasin haka ya faru ya uwargida za ta tunkari wannan matsala? To a gaskiya fuskantar wannan yanayi dole sai Uwargida ta hada da dabaru iri daban-daban.
Idan uwargida Allah ya hada ta da mijin da bai iya zaman hira ba to fa akwai wasu halayya da dabi’u da za ta koya saboda samun zama mai dorewa. Akwai hanyoyi da dama da uwargida za ta bi domin shawo irin wannan matsalar.
Abu na farko shi ne uwargida dole ta zama mai hakuri domin kuwa abin da hakuri bai ba da ba rashin shi ba zai ba da ba. Idan uwargida ta fahimci mijinta mutum ne da bai iya zaman hira da mace ba to abin da za ta fara yi shi ne daga ya dawo gida ya zauna da ma Uwargida ta tabbatar da ta tanadi labarai da za ta yi wa maigida wanda suka hada da na nishadi da kuma na ban al’ajabi,
Idan uwargida na son hira da miji ba fa daga dawowansa za ki sake ki fara zuba ba, ki karanci yanayin fuskar sa tukunna in yana cikin walwala to da ma labarai da za ki bayar su kasance na nishadi da barkwanci in kuma ta ga yanayinsa na rashin jin dadi ne to labarai ta za su kasance na tausayi da kuma darussan zaman duniya.
Kar uwargida ta ce kullum ita kadai take abu daya ta gaji, haka nan za ki daure ki ci gaba dama ai ibada akwai wahala saboda haka uwargida ta dauka wani jihadi ne za ta yi.
Sannu a hankali uwargida za ta cimma riban abin da take nema. Da yawa gidan aure rashin hira shi ke haddasa rashin jituwa a tsakanin uwargida da maigida saboda hira abu ne da ke kara shakuwa da soyayya a tsakanin ma’aurata.
Yawanci sai ka ga gidaje ana zaman ko in kula tsakanin uwargida da maigida ya dawo aiki ya shige daki ke kuma uwargida kin hakimce a falo kin sa Talabijin a gaba kina kallo, to ba haka ake yi ba ko da a ce ba mai son hira ba ne mijinki, bi shi ki karanci yanayinsa, kirkiro tadi da haka tun kina yi ba ya ansawa har ya zo ya fara ansawa gaba-gaba sai ki ga da kanshi ya fara bude baki yana magana, sai dai fa uwargida ba za ta cimma wannan nasara ba har sai ta hada da kalmar nan da ta dade tana ji wato’ HAKURi’.
Rashin zaman hira da miji yana haddasa rashin jituwa ko dan yaya ne, uwargida ta daure ta dinga jefo magana daya tare da amfani da ilmin kissa da Allah ya ba ta tana yi, tana yi har ta cimma nasara ya fara tanka mata.
Shi fa namiji kamar karamin yaro yake, yadda kika masa tarbiyya haka za ku tafi da shi, in kika masa daya kafin a kai ga na biyu zai amsa miki, kar ki ce kin gaji, daure ki jajirce saboda akwai mijin da shi fa bai iya hira ba, bai san ta ina zai fara ba amma in kika fara dago masa sai ki ga kun ja awanni kuna tadawa. Hira da miji kan sa uwargida ta fahimci ina suka dosa a zaman auren su.
Na san da yawa mata za su ce su fa sun gaji ba za su iya suna magana ana amsa musu da eh ko a’a ba, kar ki gaji, wannan amsawar da yake yi za ki ga ribarta wata rana saboda duk ranar da kika yi shiru sai ya ji ba dadi saboda ya saba sai ki ga daga nan ya bude bakinsa.