Tun bayan lokacin da aka naɗa shi, a matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa Ta Ƙasa NPA, Dakta Abubakar Ɗantsoho ke kai gworo da mari, wajen ganin ya farfaɗo da ƙima da kuma darajar NPA.
Wannan namijin ƙoƙarin da Ɗantsoho ke ci gaba da yi, na ɗaya daga cikin ƙudurin Shugaba Bola Tinubu, na Renewed Hope Agenda, musamman domin Gwamnatin ta Tinubu, ta samar da sabon sauyin da zai inganta ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, yadda za su tafi kafaɗa da kafaɗa, da sauran na duniya.
Domin a cimma nasarar wannan ƙudurin na Gwamnatin Tinubu ne, Ɗantsho ya ƙirƙiro da sauye-sauye da dama da suka haɗa da, samar da kayan aiki na gyaran Tashoshin na zamani na biliyoyin dala, musamman domin a sauya tsaffin kayan Tashoshin da kayan aiki na zamani.
- NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta
- Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi Haɗin Gwiwa
Kayan aikin na zamani da za a yi aikin da su a Tashoshin waɗanda ake sa ran wanzar da su bisa bin ƙa’ida da kuma burin ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasar, ba wai kawai manufar ke nan ba, har da sake dawo da fata da kuma ɗora fannin yadda zai kai ƙara kai wa wani babban mataki na ci gaba, a fagen hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka.
A ƙarƙashin dokar ƙasa ta 155 aka kafa NPA ne, wadda a 1969 tun da farko hukumar na kula da kawai Tashoshin Jiragen Ruwa na jihar Leg as da kuma ta garin Fatakwal.
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya.
A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli da dama, sun dabaibaye NPA da suka haɗa da, cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki, musamman na zamani da sauransu, inda waɗannan matsalolin suka haifar wa da NPA koma baya matuƙa, musamman na wajen zama a kan gaba wajen gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka.
Amma, za mu iya cewa, Allah san barka da naɗa Dakota Abubakar Ɗantsoho, a matsayin zaƙaurin shugaban hukumar kuma mai hangen nesa, wanda ya a baje ƙwarewarsa da kuma hazaƙarsa da su yi daidai da ƙugurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake farfaɗo da fatan ga ƴ an ƙasar da kuma ita ƙasar Kant’s, wato Renewed Hope Agenda.
Ɗantsoho, da shigarsa ofis, bai wani ɓata lokaci ba, ya fara da ƙaddamar da gagarumin bincke domin gano inda ake da giɓi kan gudanar da ayyukan a NPA wanda hakan ya ba shi damar, yin garanbawul baki ɗaya a hukumar, musamman domin ya sake ɗora ta, a kan turba, mai ɗorewa.
Domin tabbatar da ya daƙile ƙalubalen cunkoson musamman na Jiragen Ruwa da ke sauka, Ɗantsoho ya yi ƙoƙari wajen ganin, an yi nesa da hanyoyin Tashar Jiragen Ruwa ta jihar Legas da Tashoshin Jiragen Ruwa na Fatakwal da ta Onne da ta Warri da kuma ta Kalaba musamman duba da cewa, rashin ɗaukar wannnan matakin tun da farko a baya, ya haifar da cunkoso da ya kai kaso 90
Kazalika, baya ga magance wannan matsalar ta cunkoso da shugaban ya yi,hakan ya kuma sanya hada-hadar kasuwanci a yankunan da ke a nahiyar Afirka, ƙara tunbatsa.
Ɗantsoho, bai tsaya a nan ba,misali saboda tsaikon da ake samu a Kogin Riba Neja, ya ƙirƙiro da aikin yashe hanyoyin ruwan, musamman domin a rage cunkoso da ake samu a Tashar Jiragen Ruwa ta Onitsha, wanda hakan ya taimaka wajen ci gaba amfana da albarkatun tattalin arziki.
Bugu da ƙari, saboda burin da ya ke da shi, musamman na zamantar ƙufurin ƙara ciyar da hukumar gaba, Ɗantsho ya tabbatar da an ware dala biliyan ɗaya domin a yiwa ginin Tashar Jiragen Ruwa ta Tincan Island da ta Apapa da ta, Riɓers da ta Onne ta ta Warri da kuma ta garin Kalaba.
Asusun Bunƙasa Ayyuka wato RHIDF ne, ke tallawa wajen gudanar da waɗannan ayyukan wanda hakan ɗai ƙara taimaka wa wajen ƙara bunƙasa ɗuba hannun jari a fannin.
Hakazalika, a ƙarƙashin iya salon shugabanci na gari na Dakta Ɗantsoho ke ci gaba da gudanarwa, an samu raguwa cunkson Jiragen Ruwa da sauka a Tashshin da suka kai kaso 45.1 da kuma samun ƙaruwar shigo da Kwantainoni, da suka kai kaso 9.7 wanda hakan, ya ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci natuƙa.
Ɗantso ya kuma ƙirƙiro da tsarin yin amfani da na’urar Electronic truck call-up wanda hakan, ya ƙara zamantar da ayyuka a Tashohin Jiragen Ruwan tare da kuma rage cunkoso, Jiragen Ruwa.
Ɗaukacin waɗannan ayyukan da Ɗantsoho ke gudanawar, sun zo ne, daidai da manufar gwamnatin shuigaba Bola Tinubu.
Shugaban na NPA ya kuma kasance a kan gaba wajen ganin an ƙaddamar da Tashin Tsayawar Jiragen Ruwa na kan tudu, kamar dai, na gain Funtuwa, da ke a jihar Katsina, wnada an yi hakan ne, domin ƙara haɓaka fitar da kana da ba su shafi fannin Mai ba da kuma ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci.
Shirin aikin kashe dala biliyan ɗaya a Tashar Snake Island wanda za a ƙara faɗaɗa kadada 85 a cikin Tashar, an yi ne, bisa nufin gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a Tashar, wanda hakan zai kuma ƙara ɗaga darajar Nijeriya a fagne kasuwanci.
Ayyukan ci gaba da Ɗantsho ke ci gaba da samarwa a NPA, ba wai kawai nan ya tsaya ba, domin kuwa, a kwanan baya, an zaɓe shi ya zama shugaban ƙungiyar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya wato PMAWCA.
Wannan zaɓar ta sa, ta nuna a zahiri, irin tunbatsar da ficen da ƙasar nan ta yi a fagen na harkar sufurin Jiragen Ruwa, musamman a nahiyar Afirka
Har ila yau, Ɗantsho shugaba ne, da bai yin wasa da kula da walwalar da haƙƙoƙin ma’aiakatasa, musamman domin ya tabbatar da yaƙi cin hanci da rasahawa.
Duk dai a ci gaba da marawa tsarin shugaba Tinubu na ci gaba da ƙara tarawa ƙasar kuɗaɗen shiga, Ɗantsoho ya amince da kafa tsarin tara kuɗaɗe shiga na kai tsaye, a NPA ta hanyar yin haɗaka da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta ta ƙasa wato NIMAS da kuma hukumar Kwastam.
Wannan manufar, an yi ta ne, domin a tabbatar da ana bin diddigin tara kuɗaɗen shigar da kuma kula da su.
Ɗantsoho, ya kuma tabbatar da ana ƙara ƙarafafawa masu hada-hdar Jiragen Ruwa na ƙasar guiwa wanda kuma ya yi daidai da manufar gwamnatin ƙasar.
Burin da har zuwa yau Ɗantsoho ya sanya a gaba shi ne, ganin NPA ta tsarewa tsara, wajen ƙara samar da ci gaba ba wai kawai a tsakanin nahiyar Afirka ba, har a ma faɗin duniya.














