Cikin shekara guda da ’yan watanni da na yi a kasar Sin, kusan zan iya cewa, bikin da gwamnatin kasar ta shirya na karshen shekara ga kwararru da ke aiki a kasar, ya zamo kan gaba a sahun abubuwan da suka fi kayatar da ni.
Ba biki ne na ciye-ciye da lashe-lashe da tande-tande ba, hasalima, ko ruwan sha ba a amince a shiga da shi zauren bikin ba. Amma kuma gamsuwar da ni na samu, har ma ta hana ni jin kishi bare yunwa. Duk da cewa, an saba shirya irin wannan biki a wasu wurare ta hanyar gudanar da liyafa, amma na kasar Sin sai ya zo da wani sabon salo wanda ya kunshi ilmantarwa, fadakarwa da kuma nishadi. Babban jigon bikin shi ne nuna yadda wani mai basirar fenti a zamanin Daular Song ta kasar Sin, Wang Ximeng (wanda ya rayu tsakanin shekarar 1096 zuwa 1119 miladiyya) ya yi fenti na zanen koguna da tsaunuka, lokacin da yake matashi dan shekaru 18 da haihuwa. Yanzu haka, wannan fentin nasa mai tarihin fiye da shekaru 900, yana nan a gidan tarihi na fadar sarakuna dake birnin Beijing, kuma har yanzu bai kode ko lalace ba.
Cikin kade-kade da bushe-bushe da raye-raye, hazikan matasan da suka nuna bajinta wajen ba mu wannan tarihi, suka bayyana mana yadda matashin ya samu nasarar yin fentin daga farko har karshe. Daga abubuwan da suka fi kayatar da ni a cikin tarihin akwai jajircewar matashin, da yadda yake tafakkuri cikin dare, sannan da yadda karfin niyyarsa ta ba shi damar samun wasu abubuwa da yake bukata. Kazalika, yana da wani muridi mai kokari da ya rika tallafa masa tare da karfafa shi a duk lokacin da gwiwarsa ta yi sanyi. Kana uwa-uba, ya yi fentin ne saboda al’umma ba don kansa ba, wanda a gaskiya, yayin da aka nuna yadda shi da muridinsa suka ji dadi har suka yi kukan farin ciki lokacin da suka ga mutane sun zo kallon fentin kuma suka nuna jin dadi, ni ma dai sai da kwalla ta zubo min.
Akwai darussa da dama da za a koya daga tarihin Malam Wang Ximeng. Sannan matasan da suka yi bayar da tarihin cikin salon wasan kwaikwayo, sun nuna kwarewa matuka, domin duk wani motsi da suka yi, ya kasance mai ma’ana, inda hakan ya sa duk da kwashe kusan sa’o’i uku ana wasan, mutane ba su nuna gajiya ko kosawa a kamala ba.
Ma’aikatar kula da harkokin al’umma ta kasar Sin ce ta shirya wannan biki domin nuna godiya ga kwararru ’yan kasashen waje dake aiki a kasar Sin, bisa gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














