• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Farfado Da Tsohon Birnin Khiva

by CGTN Hausa
2 years ago
Khiva

“Ina so in ba da jakar zinare, don kawai in kalli Khiva.” Wani tsohon karin magana na Tsakiyar Asiya ya bayyana daukakar wannan tsohon birnin mai tsawon tarihin shekaru dubu a baya. Wannan muhimmiyar tashar da ke tsohuwar hanyar siliki ta kasance wurin da ‘yan kasuwa ke taruwa, lamarin dake kiyaye wadatar wannan hanyar kasuwanci mai tsayi.

A shekarar 2022, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasar Uzbekistan karo na uku, ya mika wa shugaban kasar Shavkat Mirziyoyev wata kyauta ta musamman ta kasa, wato karamin samfurin tsohon birnin Khiva da kasashen Sin da Uzbekistan suka yi wa kwaskwarima tare. Bayan wannan kyautar kasa akwai wani kyakkyawan labari game da yadda ake sa kaimi ga mu’amalar wayewar kai tsakanin Sin da Uzbekistan ta hanyar gudanar da diflomasiyya da shugabannin kasashen biyu ke yi.

  • Sin Da Wasu Kasashe 80 Sun Yi Kira Da A Kyautata Tsare-tsaren Tallafawa Tsoffi
  • Jama’a A Fadin Kasar Sin Na Bikin Ranar Kafuwar Kasar Yayin Da Suka Shiga Lokacin Hutu Mai Tsawo

Tsohon birnin Khiva shi ne aikin kiyaye al’adun gargajiya na farko da kasar Sin ta aikata a tsakiyar Asiya. To sai dai kuma saboda rashin gyare-gyare, wasu tsoffin gine-gine a tsohon birnin na ci gaba da tabarbarewa har ma suna gab da rugujewa.

A cikin shekaru shida da aka yi hadin gwiwa tsakanin Sin da Uzbekistan wajen gudanar da aikin gyare-gyaren, “likitocin kayayyakin al’adu” na kasar Sin sun yi aiki kafada da kafada da jama’ar kasar don maido da tsoffin gine-gine ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tare da yin iyakacin kokari wajen kiyaye gaskiya, da kuma cikakkun bayanan tarihi masu daraja na tsohon birnin Khiva.

“Ana yin mu’amalar wayewar kai ne saboda kasancewar bambance- bambance, ana koyi da juna ne saboda yin mu’amala, ana kuma samun ci gaba ne saboda a koyi da juna.” “Ba wai kawai mun sanya wayewar kanmu mai cike da kuzari ba, har ma mun samar da yanayi mai kyau don ci gaban wayewar kan sauran kasashe, ta yadda lambunan wayewar kan duniya za su kasance cike da furanni.” A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashe 17 bisa raya shawarar “ziri daya da hanya daya” don gudanar da ayyukan binciken kayayyakin tarihi guda 33 na hadin gwiwa, tare da sa kaimi ga hadin gwiwa a fannin kiyayewa da gyare-gyaren kayayyakin tarihi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Matar Sir Alex Ferguson, Carthy Ferguson Ta Rasu

Matar Sir Alex Ferguson, Carthy Ferguson Ta Rasu

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.