Isa Abdullahi Gidan Bakko" />

Yadda Aka Yi Jana’izar Iyan Zazzau A Zariya

A jiya Asabar aka yi jana’izar marigayi Iyan Zazzau Alhaji Muhhammad Bashari Aminu a babban masallacin Juma’a na Sabon garin Zariya, inda al’ummar musulmi da kuma sauran al’umma suka halarta.
Marigayi Iyan Zazzau ya rasu ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 31 da kuma jikoki ma zada da mata ma su
yawan gaske.
Marigayi Iyan Zazzau day a fito daga gidan sarautan Katsinawa kuma daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu da ya shafe shekara goma shatara a karagar Zazzau, ya fara karatun firamare a makarantar firamare ta L.E.A AMINU a Sabon garin Zariya daga nan bayan ya kammala firamare sai ya sami shiga Kwalejin Alhudahuda da ke birnin Zariya, ya na kammalawa sai kuma ya sami shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Marigayi Iyan Zazzau ya na da digirin farko da na biyu a fagen ilkmin kididdigan kudi da duk ya samu a wannan Jami’a ta Ahmadu Bello, kuma ya sami damar yin kwasa – kwasai a wannan fage na kididdigan kudi a kasashen da suka hada da Amuruka da Birtaniya da sauran kasashe da dama .
Marigayi Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu ya fara aikin gwamnati a kwalejin koyon tukin jiragen sama [ NCAT ] da ke Zariya a matsayin babban akawun wannan kwalejin da aka ambata.
Bayan an kammala yi ma sa sallah bisa jagorancin babban Limamin Zazzau, Alhaji Dalhat Kasim Imam, al’umma da suka hada da yayansa Wamban Zazzau Alhaji Abdulkarim Aminu, kuma hakimin Giwa, ya sifanta dan uwnsa da cewar mutum ne mai girmama na gaba, a cewarsa ba su taba gardama ba ko dad a rana, ya ce a matsayinsa na mai shekaru fiye da na marigayin, duk abin da zai yi in dai ya shafi zumunci, sai ya tuntube shi kafin ya yanke hukumci.
Wamban Zazzau ya ci gaba da cewar, ba kowa ya san halinsa na saukin kai ba sai wanda ya kasance a kusa das hi, wato shi mutum ne mai sauraron kowa da kowa ba sai wanda ya sani ba, ya ce baa bin da zai ce sai Allah ya gafarta ma sa, ya kuma share kura kuransa da ya sani da wanda bai sani ba.
Sauran wadanda suka yi tsokaci kan rasuwar marigayi Iyan Zazzau sun hada da wani jagoran ibo da mai suna Mista Cif Friday Onibuchi, ya bayyana marigayin da cewar, shugaba ne nagari da duk wanda ya san shi ya san mutum ne mai hada kan al’umma da kuma tallafa ma su, a duk lokacin da bukatar haka ta taso, ya kara da cewar, shugabancin da ya yi ba al’ummar Zazzau ne ke amfana da shi, duk wata kabila ta je wajensa, ya na yin duk abin da zai iya, na ganin ya faranta ma sa rai ba tare da nuna wata dagawa ba.
Al’umma da dama da wakilinmu ya sami damar zantawa das u sun bayyana cewar, rasuwar sa targade ga al’umma da dama, musamman in an dubi yadda ya yi fice wajen daukar rayuwa da hidimomin al’umma, wannan ne ya sa a cewarsu, rashi ne da ta sami babban gurbi a zukatan al’umma daban – daban da suke ciki da wajen jihar Kaduna.
In mai karatu bai manta ba marigayi Iyan Zazzau ya na cikin wadanda suka nemi hawa karagar Zazzau, bayan rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji ma su zaben sarkin Zazzau sun kammala zaben sarkin ne sai Iyan Zazzau bai gamsu da hanyoyin da aka bi na nadin sabon sarkin ba, wannan ne ya say a kai kara babban kotu jihar Kaduna, da ked a zama a garin Dogarawa, wanda zuwa hada wannan rahoton kuma Allah ya karbi rayuwarsa, kuma batun wannan shari’a na gaban babban mai shari’a Kabiru Dabo
Kuma a ranar goma sha biyar ga wannan wata na Janairu shekara ta 2021, kotun za cigaba da sauraron wannan kara inda za ta sauraribangarorin da suke da hannu wajen zaben sabon sarkin Zazzau.
Zuwa hada wannan rahoto, al’umma na ci gaba da zuwa gidansa domin yi wa iyalansa ta’aziyyar wannan babban rashi na Iyan Zazzau Alhaji Muhammadu Bashir Aminu.

Exit mobile version