Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Ado Mata
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake Faten Acca:
Abubuwan da ake bukata:
Acca, Nama,Tattasai, Tumatur, Mai, Albasa, Magi, Gishiri, Kori, Tayim, Citta, Black pepper, Ganye:
Yadda za a hada:
Da farko za ki wanke Acca sai ki fid da kasar sai ki ajiye waje guda,
Sannan ki sanya mai a tukunya idan ya yi zafi sai ki sa albasa wadda dama kin gyara ta kin yanka ta sai ki zuba ki soya ta sama-sama ta dan yi ja, sannan ki kawo kayan miyanki wanda dama kin gyara su kin jajjaga su ki zuba ki soya, sannan ki zuba magi, gishiri, kori, tayim sai ki zuba ruwa daidai yadda kika san zai dafa miki ya dahu sannan ki zuba nama sai ki rufe ki bar shi naman ya dahu.
Sannan ki zuba Acca sai ki gauraya ta ki bar ta ki rufe ta na dan mintoci haka ta ci gaba da dahuwa za ki ga tana tukewa.
Da kin kusa saukewa sai ki zuba ganye, za ki yi amfani da duk ganye da kike so, wanda dama kin yanka shi kin wanke, sannan ki juya shi ki rage wuta sosai ki dan bar shi ya dan dahu sai ki sauke. A ci dadi lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp