Assalamu alaikum, Barkanmu da sake saduwa cikin shafinmu mai albarka na sana’a sa’a.
Yau za mu yi magana ne akan yadda ake hada kayan kamshi na miya. Wannan ma sana’a ce dake da riba biyu, ga ta lafiyar jiki gashi kuma ba ya wuyar yi, sannan kuma ba sai da jari mai yawa ba wato bai bukatar jari mai yawa, bugu da kari, ba ta daukar lokaci wurin hada ta.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Magidanci Da Iyalansa Da Makwabta A Abuja
- Sama Da Masu Amfani Da Kayayyakin Laturoni Miliyan 20 Ne Suka Nemi Tallafin Musayar Kayan Laturoni
Kayan kamshi na miya na da kyau sosai. Yana sa miya kamshi kuma yana karawa jiki lafiya, amma fa wanda aka hada shi da kayan itatuwa. Mace in ta cika mace ya kamata a ji kamshi a girkinta, kuma sana’a ce mai riba sosai don ko ina ana amfani da kayan kamshi na girki.
Abubuwan da Ake Bukata Don Hada Spices su ne:
Citta, Na’a’na’a, Tumeric, Lemon Grass, Starus, Garlic wato tafarnuwa (busasshiya) Masoro, Kanumfari, Kwaranjal, Girfa, Shamat, Hub Zara, Bakin Algarib, Roba, (container), cokali (for midture)
Ga kuma yadda Ake Hadawa:
Da farko za ki dauki tumeric din da kika siyo a kasuwa,ki jika shi ya jiku, za ki bar shi ya kwana a jike, idan ya kwana, za ki ga ya taso, sai ki wanke shi da soso sosai zai yi fari, ki shanya shi ya bushe.
Sai ki nemi Mazubinki mai kyau, ko roba ko kwano da ba ruwa a ciki ki zuba, ki dauko lemon grass ki zuba, ki dauko citta ki zuba akan kayan kamshin, ki dauko masoron ki, Akwai masoro kala biyu akwai wanda za ki gan shi shafal-shafal akwai kuma wanda aka soya wato soyayyen masoro da shi ake amfani wurin hada kayan kamshin saboda ya fi kamshi.
Ki dauko Na’a na’a, Kirfa, Shamar, Kwaranjal, Kanumfari,Yanasun, Hub zara, Starus ki tabbata kin daka ta ta fita daga kundu-kundunta, busasshiyar tafarnuwa,Bakin Algarib duk ki Hada su wuri daya don kai nika.
Ki tabbata kin markada shi ya yi laushi sosai idan nikan bai yi laushi ba za ki iya tankade shi sai ki samu mazubin ki mai kyau sai ki sa a cikin robobin na ki na sayarwa. Shi kenan kin gama.
To za ki iya buga sticker a jikin robar duk don kara armashin sana’ar.
Ma su karatu kun ga wannan dai an yi amfani da sinadarai dake kara lfy da kuma gina jiki.kuma ba ya baci ba kamar wasu na kanti ba da ke iya janyo cuta ba saboda chemical.