Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
Sai a zo yadda za a shimfida Nori.
A shimfida takardar nori a kan tabarma ko roba mai laushi (ko wrap).
Sai shinkafa a kai (kusan ¾ na nori) ku matse da hannunku, sai ku bar gefe kadan a sama saboda likawa daga baya.
Sannan cikewa:
A jera kwakwamba, kifi, abocado, ko duk abin da kuka zaba.
Kada ku cika sosai don kada ya warware.
Sai Nadewa:
Da taimakon tabarma, za a fara nadewa daga kasa sannan a yi sama.
A matsa sosai yayin nadewa don ya daure sosai.
Idan kuka kai karshen nori, ku dan shafa ruwa ko binegar a bakin domin ya likewa.
Yankewa:
Sannan a yanke cikin kanana da wuka mai kaifi. Ku jika wukar da ruwa kafin yankewa don kada ya manne.
A Jika da miya:
Sai a ci da miyar jajjagen da kukayi. Aci dadi lafiya.
Shawara:
Idan bakwa son kifi za ku iya amfani da nama da aka dafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp