Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake dahuwar Shinkafa da Kwakwa a hade
Abubuwan da ake bukata:
Shinkafa kofi 2, Kwakwa guda daya ko coconut milk kofi daya ko biyu, Tumatir dan kadan ba dole bane, Albasa daya, Man gyada ko man Zaitun, Kori da Tayim, Magi, Gishiri, koran wake, Karas, koran tattasai amma ba dole ba ne, naman kaza ko kifi idan ana so.
Yadda Ake Hadawa:
Da farko za a fasa kwakwa sai a fitar da ruwan kwakwar, sannan sai a bare ta, a dan yayyanka ta sai a nika ta a sa dan ruwa kadan haka, nikan ya yi laushi sosai. Sai a tace ta, a fitar da ruwan daban.
Sannan a wanke shinkafa a jika na dan wani lokaci, a yanka albasa, sai a dauko tukunya a zuba man gyada a soya albasa har ta yi laushi, sannan sai a zuba kori da tayim sai a zuba ruwan kwakwa coconut milk, a saka magi da gishiri,
A zuba shinkafa a gauraya a barshi ya tafasa. Sai a zuba koran waken da tattasai da tomatir wanda dama an gyara an yanka su ko an jajjaga duk wanda mutum yake so, a tabbatar kome ya ji sai a zuba naman wanda dama kin tafasa kuma kin soya sai a barta ta dahu. A ci dadi lafiya.














