Iyalan Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Abdullahi Bello Boɗejo sun koka kan sake kama shi da jami’an Hukumar tsaron farin kaya DSS ta yi a ranar Juma’ar nan, bayan bada belinsa da Hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasar EFCC ta yi.
Shugaban na Miyetti Allah na fuskantar shari’a ne a gaban wata kotun tarayya kan zargin halatta kuɗin haram, biyo bayan gurfanar da shi a gaban kotun da Hukumar EFCC ta yi, inda kotun ta bada umarnin bada belinsa a ranar 20 ga watan da ya gabata, bisa wasu sharruɗa.
Ta ce, “Hukumar ta EFCC ta kira su ta waya a ranar Alhamis da daddare, tare da buƙatar da su bayyana a ofishinsu a ranar Juma’a ciki hadda jami’an na kotu, don Karɓan belinsa daga hannunsu,” in ji ta.
“Kotun ta bayyana mana cewa, babu buƙatar sake komawarsu zuwa hedikwatar Hukumar ta EFCC, bayan nan ne sai muka garzaya ofishin na EFCC a ranar Juma’ar inda ta saki maigidana a bisa matsayin beli.”
Sai dai fitarmu daga ofishin ke da wuya, sai jami’an DSS, da muka iske a babbar ƙofar ofishin, sai suka sake kama shi tare da garzayawa da shi zuwa cikin ɗaya daga cikin motocinsu guda uku da su ajiye a wajen da su, sannan suka wuce da shi, in ji Hajiya Hauwa, Mai ɗakin ta shugaban na Miyetti Allah Kautal Hore, ta kuma sake bayyana buƙatar na iyalan na Boɗejo na neman a yi masa adalci a shari’ar da ake yi masa.
Ta yi ƙorafin cewa, mai gidan nata ya na fama da matsalar rashin lafiya sannan kuma bai samu damar ganawa da likitansa ba, a tsawon wata uku da yake tsare a halin yanzu, kamar yadda ta bayyana.














