Duba da yadda ake kyankyashe kwan kaji, ba kowa ne zai iya yi ba, amma idan kana so ka koya to ga yadda ake yi; da zarar Kajin sun yi kwai, sai ka kwashe su daga wurin da suka yi kwan, musamman ganin sukan danne kwaikwayen har su fashe.
Wannan dalilin ne ya sa, masu yin kiwon Kaji a gidajensu da kuma sauran masu kiwon Kajin, suka gwammace su kyankyashe Kajin da kansu. Idan kana so, za ka iya sayo ‘yan Tsaki haihuwar kwana daya, in ba ka so ka kyankyashe su da kanka; amma fa sun fi tsada.
- Dalilan Karancin Kajin Gidan Gona A Nijeriya
- Abubuwan Da Ke Rusa Masana’antun Kiwon Kaji A Nijeriya
Matakin Farko: Kafa Injin yin kyankyasar, wanda wannan ya danganta da yawan Kwaikwayen da Injin kyankyasar Kajin zai dauka, akasarin wasu Injinan na daukar Kwai kamar hamsin, inda kuma idan kyankyasar ta kasuwanci ce, wasu injinan kyankyasar na daukar yawan Kwaikwayen da suka kai dubu guda. Don haka, za ka bude injin ka saka Kwaikwayen a cikinsa ka rufe kofar injin kyankyashar Kwaikwayen.
Har ila yau, ana so ka tabbatar ka wanke hannayenka kafin ka dauki kwaikwayen, ka zuba su cikin injin kyankyasar; don gudun lalacewa.
Sannan, ana so yanayin injin kyankyasar ya kasance daga yanayi 50, 60, ko 75.
Yanayin Da Ya Fi Dacewa Da Kyankyasar: Ana bukatar zuba Kwaikwayen a cikin injin, wanda yanayinsa ya kai digiri 99.5 a kowane lokaci, amma idan ya zarce wannan adadin ko kuma kasa da haka, zai iya lalata ruwan da ke a cikin Kwan.
Haka zalika, ana so zafin cikin Injin kyankyasar ya kasance ya kai kamar 50 cikin dari, inda ake so a ci gaba da tafiyar da shi a hakan har zuwa tsawon wasu kwanaki.
Bugu da kari, kafin Kwaikwayen su fara kyankyashewa, ana so zafin cikin Injin ya kasance daga daga kashi 65 zuwa kashi 75 a cikin dari.
Mataki Na Biyu: Ana bukatar wanda zai yi kyankyasar Kajin, ya tabbatar ya samo ingantattun Kwaikwayen yadda hakan zai sa kyankyasarsu ta yi kyau.
Ana bukatar da zarar sun yi Kwan, a kwashe su a zuba a cikin Injin kyankyasar, idan kuma ba a da Kwayayen, za a iya sayowa.
Mataki Na 3: Kwan na kai wa kwana 21 kafin kyankashewa, sannan kafin a saka kwaikwayen a cikin injin, ana so a tabbatar da yanayin zafin injin tare da daukar akalla sama da awa 24 da kunnawa, sannan a zuba a kyankyshe su.
Kana a tabbata ana juya kwaikwayen a lokacin da suke cikin injin kyankyasar, kamar sau uku ko biyar ko kuma bakwai.
Haka nan, ana bukatar a ci gaba da juya su har zuwa kwana 18, daga baya kuma sai a kyale su har zuwa tsawon wasu ‘yan kwanaki.
Mataki Na 4: Idan sun kyankyashe, a cikin injin za a ga kwaikwayen na motsawa, wato a wannan lokacin ne za su fara yin numfashi.