Yadda Ake Soya Kaza Da Fulawa Da Kwai

Daga Bikisu Tijjani,

Abubuwan da uwargida za ta tanada: Kaza, Fulawa, kwai, Magi, Gishiri, Kuri, Albasa da mai.

Yadda uwargida za ta hada:

Za ki wanke kazarki bayan kin gama wankewa sai ki dauko tukunya ki zuba ta a ciki ki sa mata ruwa dan kadan yadda za ta tsose ruwan a jikinta saboda komai ya shige ta, sannan ki sanya mata gishiri yadda kika ga zai ishe ta, sai ki sa mata magi shi ma daidai yadda zai isa, daga sai ki sa albasa mai dan yawa saboda gudun karni, za ki dan iya sa ‘yar citta ita ma za ta taimaka wajen cire karni, amma ba sai kin daka ta ba idan kin samu danya za ta fi, sannan ki sa kuri kii dorata a wuta, sai kii barshi ya dan yi kamar mintuna ya danganta da yanayin kazar idan mai tauri ce.

Amma fa ba’a son kazar ta dafe, ta tafasa dai haka yadda ba za ta yi tauri ba kuma ba ta dahu sosai ba yadda fatar ta za ta cure ba, idan ta yi haka sai ki sauke kina sauke ta sai ki kwashe ta a tukunya, ki zuba ta a matsami saboda ta tsane ruwan jikinta, sannan ki dauko abin suya ki zuba mai a ciki ki dora shi a wuta ki dan sa masa albasa kadan saboda ya yi kamshi, sai ki dauko fulawarki ki zuba ta a wani firanti ko roba, sannan ki dan sa wa fulawar gishiri kadan da magi da kuri ki gauraye ta, sai ki samu wani dan kwano ko roba ki fasa kwai a ciki daidai yadda kwan zai ishi kazar, sai ki dan sa masa gishiri kadan da magi.

Amma kadan kadan sannan ki dauko kowane yanka na kazar ki dinga sawa a cikin kwan ki juya shi ko ina ya taba kwan a jikin kazar, ki jijjuya ta sannan ki cere ta ki sa ta cikin fulawar ki barbada fulawar a cikin kazar ki jijjuya ko, ina fulawar ta kama jikin haka za ki yi ta yi har kazar ta kare, bayan kin gama yaba musu fulawa da kwai, sai ki fara soya wa kina daukarsu kina sa wa a cikin man da kika dora haka za ki jera su a cikin abin suyar, daga nan sai ki bar su ki dan bata kamar minti biyar zuwa goma kina dubawa idan kasan ya yi kalar kasa-kasa sai ki juya ta saman ya koma kasa don shi ma ya soyu, haka za ki ta yi har ki gama.Idan kin yi wa maigida laifi ai da ya ci wannan kazar ya manta da laifin, A ci dadi lafiya.

 

 

 

Exit mobile version