Ci gaba daga makon da ya gaba ta
Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai ci gaba da koya mana yadda ake hada Pizza a gida:
Abubuwan da ake bukata:
Dough, Tomato paste, Cuku, Kaza, Kayan miya.
Yadda ake hadawa:
Da farko za a shimfida dough a kwanon gasashe, sannan sai a shafa tomato paste a saman, sai a zuba cuku a matsayin layi na farko sai a yanki kaza wadda dama an riga an tafasa ta da kayan dandano a zuba, sannan a kawo kayan miya a zuba a saman, sai a kara wani layin na cuku. A gasa na minti 15–20 a murhun gashi wato (oben), ko a soya shi a kan tanderu mai murfi idan babu oben.














