Ganin cewa Azumin Ramadan na bana ya kai karshe, a yau darashin namu zai yi bayani ne a kan Zakatul Fidir. Ma’anarta ita ce Zakkar Shan Ruwa, ita ce da Hausa wasu ke ce ma ta Zakkar Fid da Kai.
Zakkar wajiba ce a kan kowane Musulmi, yaro ko babba, namiji ko mace, da ko bawa. Ta wajaba a kan mutum da wadanda suke karkashinsa, wato wadanda ciyar da su yake kansa. Matansa da ‘ya’yansa da masu yi masa hidima wadanda yake rike da su yake ciyar da su.
- Da Dumi-Dumi: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Sallah
- Bunkasuwar Kasar Sin Mai Inganci Ta Ingiza Kwarewar Jama’arta
Bayar da zakkar ta zama wajibi ga duk Musulmin da ya mallaki abincin da zai ci shi da iyalansa na kwana da yini kuma koda mudu daya na hatsi ya ragu masa. Abin da ake nufi shi ne, idan mutum yana da abincin da zai ishe shi ci tare da iyalansa, bayan ya ware wannan sai ya kasance an samu ragowar mudu daya, Zakkar ta hau kansa. Amma wanda ba shi da shi ta fadi a kansa, sai dai idan ya samu ya bayar, ta zama kamar bashi kenan.
Amfanin Bayar Da Zakkar
Amfanin bayar da Zakkar shi ne domin mutum ya tsarkake kansa daga suratai marasa amfani ko batsar da ya aikata a cikin watan Azumin Ramadan domin ibadar da ya yi ta Azumi ta kubuta lafiya kalau. Haka nan amfaninta ya hada da ciyar da talakawa da almajirai wadanda ba su da abincin da za su ci don yaye masu kunci na rashin abincin, domin kuma kar a gan su sun fito suna bara.
An farlanta Zakkar ta Shan Ruwa ce a watan Sha’aban, bayan Hijirar Annabi (SAW) da shekara biyu.
Yadda Ake Ba Da Ita
Ana ba da ita kafin a fita zuwa Sallar Idi ko kafin Ranar Sallah da kwana daya ko biyu. Abin da ake bayarwa shi ne Muddan Nabiyy (mudun awo ne dan madaidaici wanda za a iya auna shi da cikin tafukan hannun mutum mai matsakaicin tsawo) guda hudu a kan kowane mutum. Ana fitarwa daga dukkan nau’in abinci, kamar mu a nan mu ce shinkafa, masara, doya, dawa, dauro, cukwi, nono da duk dai abin da galibin mutane suke amfani da shi a matsayin abinci.
Malaman Kasar Maroko wadda kasa ce ta Malaman Musulunci kuma ‘yan’uwanmu ne Malikawa; sun yi fatawa cewa ya halasta a ba da kudi a madadin abinci a Zakkar. Za a kimanta kudin adadin Muddan Nabiyy hudu da za a fitar sai a ba da. Wannan ya halasta.
Idan mutum ya yi nazarin hikimar ba da Zakkar, wato wadata talakawa da miskinai don kar a gan su suna bara saboda rashin abincin da za su ci a Ranar Sallah, wannan kudin da za a ba su sai ya fi musu dadi a kan tsabar abincin. Domin wani idan ka bashi hatsin watakila ba zai iya nikowa ba, toh ka ga shi a wurinsa kudin zai fi masa amfani fiye da dawa ko masara. Dan dama-dama shinkafa ko doya wanda duk za a iya dafawa ba sai an nika ba. Amma fa a lura, kowane irin abinci mutum ya bayar ya yi. Saboda amfanin kudin ne ya sa muka kawo wadannan bayanan.
An fi so a ba da Zakkar ga mutanen kirki daga cikin talakawa ko wadanda suke da almajirai a hannunsu wadanda idan an ba su ba za su je bara ba a ranar. Ita Shari’a ba ta so a ga kaskancin mutum a wannan ranar, so ake kowa ya nuna girman Musulunci, kodayake wasu ‘yan’uwa ba za su yarda ba, duk abin da aka ba su ba za su iya hakura ba sai sun fita bara. Toh amma kuma kar wannan ya sa a ce ba za a ba su ba.
Idan mutum ya fitar da Zakkar sai ya kasance babu miskinai a kusa da shi da zai ba su, to ya dauka ya kai wurin da suke ya ba su, kar ya ce ai tunda babu miskinai a kusa da shi shikenan ba sai ya ba da ba.
Fa’ida: hatta kafirin da ake zaune da shi in talaka ne za a iya ba shi Zakkar don ya wadata a wannan ranar. So ake Dan Adam ya zama ya wadata saboda albarkar ranar ta Sallah.
Sallar Idi
Sallar Idin Shan Ruwa (Karamar Sallah) da Sallar Idin Layya (Babbar Sallah kamar yadda galibin Hausawa ke cewa), an shar’anta su a Musulunci a shekarar farko da yin Hijirar Annabi (SAW) daga Makka zuwa Madina. Kuma Annabi (SAW) ya dauwama a kansu (yana aikatawa). Ya hori maza da mata da yara da manya su fita zuwa gare su, ma’ana su je Masallacin Idi.
Ana so a yi wanka, a sa turare, a sanya mafi kyan tufafi da mutum yake da shi. A Sallar Idin Shan Ruwa, ana so a ci abinci kafin a fita zuwa Masallaci koda dabino ne ko shayi. Ana so a dan jinkirta ta kadan; sabanin Sallar Idin Layya da aka fi so a jinkirta cin abinci har sai an dawo. Idan mutum ya samu ikon yin Layya; ana so ya bude baki da naman Layyar sannan an fi so a gaggauta yin ta domin a dawo gida a yi Layya.
Ba a yin Sallar Idi (duka biyun) a Rufaffen Masallaci sai dai in akwai lalura kamar ta ruwan sama. A wajen gari ake fita yin SallarIdodin biyu ko kuma duk filin da aka samu. Annabi (SAW) bai taba yin Sallar Idi a Rufaffen Masallaci ba sai sau daya saboda ruwan sama kamar yadda Hakim ya ruwaito Hadisin.
Ana so a canja hanyar da aka je Masallacin Idi wajen dawowa amma ba dole ba ne. Ana so a yi Sallar Idin Shan Ruwa kamar da misalin karfe bakwai da rabi na safe (7:30am), Sallar Layya kuma kamar da misalin karfe bakwai na safe (7:00am). Amma ko sun kai karfe goma sha daya na rana babu laifi, duk lokacin yin su ne.
Ba a yin Kiran Sallah ko Ikamah ko cewa “a tashi a yi sallah”. Da zaran Sarki ko wanda ya tsaya a matsayinsa ya iso filin masallaci sai a mike a shiga Sallah. A raka’ar farko; bayan Kabbarar Harama sai a kara Kabbara shida, sun zama bakwai kenan. A raka’a ta biyu; bayan Kabbarar Tasowa daga Sujuda sai a kara Kabbara biyar, sun zama shida kenan. Ba a yin Nafila kafin Sallar Idi (duka biyu) kuma ba a yi a bayanta. Liman zai yi huduba bayan an yi sallama, wanda yake so zai zauna ya ji wanda wani uzuri ya kama shi sai ya tashi ya tafi ba tare da ya yi magana (surutai) ba.
Ana so a yi wasanni, da kade-kade, da wake-wake, da ciye-ciye, da nishadi, da ziyarori, da yi wa juna murnar Idi. Ana so a yi kallon wasannin ko rawar da ake yi, duk ya halatta a wannan ranar. Wannan shi ne Musulunci sassauka kamar yadda Annabi (SAW) ya fada, Tirmizhi da Ibn Majah da Baihaki suka fitar.
Allah ya sa mu kammala Azumi lafiya, mu yi Sallah lafiya, ya hore wa dukkan Musulmi abin da za a yi hidimomin Sallah da shi, Allah ya karba mana ibadunmu kuma ya karbe mu da falalarsa albarkar Annabi (SAW).
Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.