Jihar Zamfara ta shafe shekaru da dama ana kiranta da jiha mafi zaman lafiya a Nijeriya, inda kabilu daban-daban ’yan asalin jihar da suka hada da Hausawa da Fulani ke zaune cikin kwanciyar hankali da lumana a tsakaninsu.
Sai dai a shekarar 2009 rashin jituwa ta fara kunno kai tsakanin Fulani da makwabtansu Hausawa a lokacin da Fulanin suka yi zargin cewa ‘yan banga da ‘yan sa-kai suna kai hari tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kasuwanni da kuma duk inda suka hadu, su kuma iyayen kasa na sayar da labi ga manoma.
- Sin Ta Zama Zakaran Gwajin Dafi A Fannin Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Tsakanin Kasashen Duniya
- Hadin Kan Sin Da Afrika A Bangaren Kiwon Lafiya Zai Ci Gaba Da Samun Nasarori
Wannnan ya sanya wasu Fulani da dama suka rasa matsuguni da wajen kiwon dabbonin su.
Ana hasashen wannan ne ya haddasa kafa kungiyar ‘yan Bindiga ta farko a Zamfara a shekarar 2011, inda suke satar shanu da fashi da makami, sannan kuma ‘yan banga na yankin suka ja layi a kan ayyukan barayin shanu da kuma kashe mutanen da suke zargin bata-gari ne.
Tun daga lokacin kauyuka har ma da wasu manyan birane na jihar suka rasa kwanciyar hankali domin ‘yan bindigar sun ci karfinsu, mata da kananan yara suka zama ‘yan gudun hijira, wadanda suka rasa wurin gudu kuma sai su zama masu biyayyar tilas ga ‘yan bindigar.
Wata majiya ta bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa sama da kauyuka 100 ne ‘yan bindiga suka mamaye a fadin Jihar Zamfara a baya, tare da kafa sansanoni kimanin 30.
Manyan ‘yan bindiga na Jihar Zamfara da rundunar sojojin kasar nan ke nema ruwa a jallo sun hada da Ado Alero, Bello Turji da Dankarami da Dogo Gide kuma duk wani ofishin jami’an tsaro an buga hotunan su shekara uku da ta wuce amma har yau ba su fada hannun hukumar ba.
Sai dai kuma, a halin yanzu akwai wasu kauyuka da suka ‘kulla yarjejeniyar zaman lafiya’ da manyan ‘yan bindigar inda da kansu suke tilasta aiki da yarjejeniyar. A shiyyar Zamfara ta Tsakiya, Ado Aleru yake jagorantar abin, sai shiyyar Arewaci inda Bello Turji da Dankarami suke nasu shugabancin, yayin da kuma a shiyyar Arewa ta Yamma, Dogo Gide ke nashi shugabancin.
LEADERSHIP Husau ta yi ta gano cewa, mazauna kauyukan da ke zama da ‘yan bindigar daga kowace shiyya, wasu na zaune lafiya da kwanciyar hankali da ‘yan bindigar, yayin da wasu kuma ke fuskantar matsaloli sakamakon rashin fahimtar juna a tsakaninsu.
A wasu yankunan, mazauna kauyukan suna zama tamkar bayi inda ake tilasta musu yin aiki a gidan shugaban ‘yan bindigar ba tare da biyansu kudin aikinsu ba sai ma kara kakaba musu kudaden haraji kafin su ba da damar yin noma a lokacin damina.
Kananan hukumomin da suka fi fuskantar barazana daga ‘yan bindigar duk da hadin gwiwarsu sun hada da; Zurmi, Gusau, Maru, Maradun, da yammacin karamar hukumar Tsafe.
Da yake bayani a karshen makon da ya gabata na yadda suke tafiyar da rayuwa tare da ‘yan bindigar, mazaunin ‘Yan Dolen Kaura da ke karkashin karamar hukumar Zurmi, Malam Aminu, ya ce yawancin ‘yan bindigar sun dora haraji nau’i daban-daban ga kowace al’umma a yankunansu kuma suna biya domin su noma gonakinsu a wannan lokacin na damina.
A cewarsa, kauyukan da lamarin ya shafa da ke kananan hukumomin Kauran Namoda da Zurmi, kimanin kauyuka 10, an dora musu harajin Naira Miliyan 15 zuwa 20, kafin a bar su su yi noma.
Ya kuma yi bayanin cewa, kauyukan da abin yafi ta’azzara an dora musu harajin kusan Naira miliyan 200 wadanda suka hada da; Gidan Duwa, Dolen Kaura, Gidan Dan Zara, Kanwa, Kaiwa Lamba, Gidan Zagi, Jinkirawa, Babani, Ruguje, Dumfawada ‘Yan Dolen Moriki.
“Hakika, haka muke rayuwa cikin zullumi, bayan sanya haraji kafin noma gonaki sannan a karshen girbi ma, ko dai ya hana mu girbin ko kuma idan muka yi kokarin ja da su, sai su harbe mu.
“Kiran mu ga Jiha da gwamnatin tarayya shi ne don Allah a kawo mana agaji domin mu ji dadin rayuwa kamar yadda wasu ke morewa a sauran sassan Jihar, mun kai ga halin da muka tsinci kanmu a halin yanzu, in ji Malam Aminu.
Shi ma Abdullahi Shamsu, wani mazaunin Gebawa da ke karkashin karamar hukumar Gusau, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa suna zaune ne da ‘yan bindiga, a cikin mumunan yanayi na rayuwa kamar yadda ya ce, wasu daga cikin ‘yan bindigar ma suna bin matansu da ‘ya’yansu mata suna yi musu fyade.
Ya ce wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga a yankin, Isah Na Shamuwa ya hana su samun kwanciyar hankali. Ya kara da cewa shugaban ‘yan bindigar wanda dan asalin yankin ne, yakan sanya su a gonakinsa suna yin noma duk rana ba tare da biyan su ba, idan kuma ka yi kokarin fadin wani abu na daban yaransa za su maka hukunci mai tsanani.
Kauyukan da abin ya shafa, sun hada da: Rijiya, Gidan Hokki, Gebawa, Ruwan Bawa, Madaro, Sakkarawa, da Bakin Dutse duk a karkashin karamar hukumar Gusau.
Binciken da LEADERSHIP Hausa ta gudanar ya kuma gano cewa, yayin da wasu mazauna kauyukan ke shan wahala a hannun ‘yan bindiga, wasu kuma daga wasu sassan kananan hukumomin kamar, yammacin karamar hukumar Tsafe da ke karkashin Ado Alero, Dogo Gide daga yankin Dansadau. Karamar hukumar Maru da Bello Turji daga karamar hukumar Shinkafi suna zaune lafiya tare da su.
An tabbatar da cewa Dogo Gide, a daminar bana ya bai wa daukacin mutanen kauyen da ke karkashinsa ‘yanci su yi noma. Wata majiya ta ce, gonaki da dama da ba a noma su kusan shekaru 7 zuwa 8 kuma suka zama dazuka a yanzu suna nan an noma su.
A cewar Alhaji Ibrahim, wani mazaunin Dansadau Hausa da aka tattauna da shi ta wayar tarho, tun da Dogo Gide, ya bayyana aniyarsa ta barin mutane su yi noma, da farko mutane sun kasa yarda suna tunanin tarko kawai ya dana musu.
“Dogo Gide, fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, bayan ya kira mutane game da noma gonakinsu, har ma ya yi gargadi ga mabiyansa cewa ka da su taba ko musguna wa duk wani dan kasa a karkashin yankinsa. Tun daga farkon damina ta bana ba a samu rahoton wani hari ko tsangwama ba kamar yadda yake faruwa a wasu shekaru ko watannin baya.
“Mutanen Dansadau, Dangulbi, Dankurmi da sauran kananan kauyukan da ba sa noma gonakinsu, yanzu suna yin noma. Wannan sabon ci gaban, ya tabbatar da cewa Allah cikin rahamarsa ya amsa addu’o’insu na ganin jihar ta samu zaman lafiya, a halin yanzu da damina mai albarka manoma za su samu girbi mai yawa a bana.” In ji shi.
Hakazalika, galibin mazauna kauyukan da ke karkashin karamar hukumar Tsafe, suna zaune lafiya tare da takwarorinsu Fulani, sakamakon kokarin Ado Alero, kuma dan asalin kauyen Hayin Alhaji, yake yi na ganin an zauna lafiya da juna, sannan kuma ya gargadi mabiyansa ‘yan bindiga da ka da su taba kowa ko cin zarafinsu.
Malam Sani mazaunin Hayin Alhaji ne, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa, suna rayuwa cikin kwanciyar hankali da ‘yan bindiga a yankin nasu.
“Ka ga a baya har ma na daina fatan cewa zan tsira, domin duk kauyenmu yana kewaye ne da ’yan bindigar Katsina wadanda suka taba zuwa da yawa a kan babura sama da dari biyu. A lokacin da suka shigo unguwarmu sai suka rika ihu suna zafafan kalamai a kan Ado Alero tare da tabbatar musu da aniyarsu ta kashe shi da mutanensa tare da yin garkuwa da daukacin al’ummarmu.
“A kan haka aka gwabza kazamin fada tsakanin kungiyoyin ‘yan bindigar guda biyu inda a karshe aka kashe ‘yan bindiga da dama daga Jihar Katsina tare da fatattakar mafi yawansu da suka tsere da raunuka.”
Shi ma wani mazaunin Hayin Alhaji, Musa Hassan, ya bayyana cewa, a lokacin da ‘yan bindigar Katsina suka iso, suka kewaye yankin, mazauna unguwar sun firgita ba tare da tsammanin kubuta daga hannun ‘yan bindigar ba, amma tare da shiga tsakani daga hannunn Ado Alero, an yi galaba a kansu kuma aka kashe su, wasu tsere suka bar babura kusan 20.
“A lokacin da fadan da aka gwabza tsakanin kungiyoyin biyu ya yi yawa, Ado Alero ya roki mutanen kauyen da su kwantar da hankalinsu ka da su tashi daga inda suke har sai fadan ya kare.
“Muna godiya ga Allah al’ummarmu suna zaune lafiya da ‘yan bindigar, ba sa cutar da mu ko yaudarar mu, haka nan muna girmama junanmu, ba mu da wata matsala da su, tare muke noma tare muke aiki a matsayin leburori,” in ji Musa Hassan.
Alhaji Nasiru Galadi daga karamar hukumar Shinkafi, shiyyar Zamfara ta Arewa, inda fitaccen dan shugaban ‘yan bindigar nan Bello Turji ya fito, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa ta wayar tarho cewa duk kauyukan da ke karkashin Shinkafi suna cikin zaman lafiya da ‘yan bindigar, sabanin watanni ko shekarun baya cikin firgita da ayyukan ‘yan bindigar a karkashin Bello Turji.
“Bello Turji shugaban ‘yan bindigar ya zama ‘gwarzo’ domin a kullum yana kare al’ummarsa da daukacin mutanen kauyen karamar hukumar Shinkafi daga duk wata cuta ko farmaki daga wasu gungun ‘yan bindiga.”
Galadi ya ci gaba da cewa, Bello Turji, a cikin wata guda yana gargadi yaransa da ka da su yi garkuwa ko kuma su kai hari a kauyukan da ke karkashinsa, kuma duk wanda ya karya doka aka kama shi za a kashe shi nan take.
Ya ce bayan fitar da gargadin, wata rana wata kungiyar da ke karkashinsa ta ki yin biyayya ga umarninsa, inda suka ci gaba da yin garkuwa da wasu mutanen kauye. Bayan wani lokaci sai Bello Turji ya samu labarin haka, nan take ya damke shugaban kungiyar tare da kashe shi.
“Hakika yanzu muna zaman lafiya da ‘yan bindigar, kuma kusan shekara guda ba mu fuskanci matsalar ‘yan bindiga ba, tun daga lokacin muna zaune lafiya, muna tafiya daga garin Shinkafi zuwa Gusau mai tafiyar kilomita 95 a kowane lokaci ba tare da samun matsala ba ko tsammanin wani hari daga ‘yan bindigar ba,” in ji Galadi.
Da muka tuntubi wasu shugabannin kananan hukumomin musamman na Birnin Magaji, Maru, Shinkafi, Gusau, Tsafe da Kaura – Namoda, sun shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, suna bakin kokarinsu wajen ganin an samu zaman lafiya a tsakaninsu.
Kananan hukumomin da abin ya shafa da ke kewaye da ‘yan bindiga, sun hada da; na Kaura-Namoda, Hon. Kasimu Sani Kaura, sai karamar Maru Hon. Yusuf Sani, karamar hukumar Birnin Magaji Hon. Isiyaka Ibrahim, karamar hukumar Maradun Hon Yahaya A. Giwa da karamar hukumar Tsafe Hon Aliyu Adamu Barmo.
A cewarsu, a kullum suna tare da mutanen kauyen, kuma ana kokarin ganin an samu zaman lafiya a yankunan da ‘yan bindigar ke yin barazana ga mazauna kauyukan a yankunansu.
Da muka tuntubi rundunar ‘yansandan jihar, kakakin rundunar ’yansandan jihar (PPRO) ASP Yazeed Abubakar, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, rundunar ta dauki kwararan matakai a Gusau da kewaye domin tabbatar da samun zaman lafiya a kowane bangare na jihar.
“Sakamakon matakan tsaro da aka dauka a jihar, an samu rahoton ayyukan ‘yan bindiga a wasu yankunan amma mun fatatake su.” In ji shi.