(1B). Sai kuma bangaren ingantatun maganin Islamic wanda lallai wajibi ne ki yi amfani da su domin maganin sanyi da duk wasu boyayyun cutuka za ki maganinsu cikin sauki tare da wankin mara gaba daya.
Gasu kamaar haka:
Habbatussauda, Hulba, Kanimfari, Kistil Hindi, Citta,Tafarnuwa, Raihan, Habbatu Rashad, Yansun, Zi’itir, Ruman, Tumeric:
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- Sin: Idan Har Amurka Na Son Tattaunawa, Ya Zama Wajibi Ta Dakatar Da Aiwatar Da Matakan Gangaci
Za ki saya ko wanne kamar gwangwani daya ko rabin gwangwani, sai a hade su waje daya a dake su ko a nika su, za ki dinga diba cokali 1 babba a kofi daya na ruwa sai ki sa zuma ko suga ki shanye kullum kafin biki da wata daya, ke a jikin kema za ki ji canji yadda za ki ji kiin samu lafiya ga ni’ima na kara saukar muki nasha-nasha.
(2). Abinci: Dole ne sai kin fara gyara daga cikin sannan ki dawo waje saboda haka abinci kowacce ya danganta da abin da kike ci ne amma dai lalle ne ki dinga cin isasshen abinci kar yanayi na makaranta ko zuwa aiki ko wani guri ya sa ki dinga fashin cin abinci domin shi abinci dole sai da shi ne duk wani sinadarai da za ki sha za su yi miki aiki saboda haka ki kiyaye sosai kuma ki dinga cin lafiyayyun abinci da za su kara fid da miki shaf.
Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin.
(2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe.
(3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji ya gama tsara ki yana ce miki kin hadu kina jin kanki kawai sai ranar daran farko za ki fara ganin canji.
Saboda haka koda bayan sa ma akwai wasu supplement da za su kara miki kyau lokacin aurenki ya kamata ki nemo asalin original ki sha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul-sumul kamar su suka yi kansu ki gansu kamar a lashe yanzu duk su suke sha shi kuma gaskiya bai da wata matsala da yawa domin suna kokari wurin inganta shi sosai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp