Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta sanar da sallamar dan wasanta na gaba Diego Costa a ranar Talata watanni 6 gabanin karewar kwantiraginsa, ba tare da bayyana dalilan da suka haddasa hakan ba.
Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta ta bayyana cewa Costa da kungiyar sun cimma jituwar kawo karshen kwantiragin da suka kulla a baya wanda a ka’ida zai kare a ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2021.
Costa haifaffen kasar Brazil mai shekaru 32 a duniya da ke buga wasa a kasar Spain ya amince da raba gari da kungiyar ne kan wasu dalilai na radin kai wanda bangarorin biyu basu bayyana ba.
Dan wasan wanda ya fara buga wasa da Atletico Madrid tun yana da shekaru 17 a Duniya, ya buga mata wasanni 215 daga 2010 zuwa 2015 da kuma 2018 zuwa 2020 bayan shafe kakar wasa 3 a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, inda ya zura kwallaye 83 ya kuma taimaka aka zura wasu 36.
Akwai dai masu ganin Costa wanda a yanzu kowacce kungiya zata iya saya ba tare da biyan kudin sallamar tsohuwar kungiyarsa ba, akwai yiwuwar ya koma buga wasa a gasar Firimiyar kasar Ingila.
Tuni aka fara danganta dan wasan da komawa kungiyar kwallon kafa ta Wolbes wadda take fama da rashin dan wasan gaba bayan dan wasanta na gaba Raul Jimanez ya samu bugu a kansa inda likitoci suka bayyana cewa kashin kansa ne ya karye.
Sannan wasu daga cikin kungiyoyin dake buga gasar firimiya kamar kungiyar kwallon kafa ta West Ham United da Fulham da kuma kungiyar kwallon kafa ta Westbrom Albion duka suna zawarcin dan wasan.