Mahdi M Muhamad" />

Yadda Budurwa Ta Kashe Kanta Akan Saurayi

Wani mahaifi a kasar Ghana ya ba da rahoton cewa zuciyarsa ta karaya bayan ‘yarsa da ya sayar da kodarsa don biyan kudin makarantarta ta kashe kanta akan saurayi.

Ba a bayyana abin da saurayin ya yiwa yarinyar ba da har ya tilasta ma ta kashe kanta ba tare da yin la’akari da wahalar da mahaifinta ya yi ba don ya sanya ta zama macen da zata amfani al’umma a nan gaba ba, kuma don ta biya masa bukatunsa lokacin da zai tsofa bai iya yin komai da kansa.
A wani labarin kuma, wata budurwa ‘yar kasar Ghana ta ce zama da saurayin ta a makabartar Osu da ke Accra babban birnin kasar ta Ghana ya sanya ta rashin tsoro domin babu wani abin tsoro.
Matar da aka bayyana suna Abena ta fadawa EyeGhana a wata hira da ta yi da ita cewa, tana tare da mahaifiyarta ne a Ablekuma, amma ta ziyarci masoyin ta wanda ke makabartar Osu.
An ruwaito ta tana cewa, mahaifiyarta ta sani game da cewa saurayin nata yana zaune a mashahurin makabartar, amma ba shi da wata damuwa game da hakan.
Ta kara da cewa, shi kansa Michael yana jin dadin zama a tsakiyar matattu kuma yana ci gaba da rokon ta da ta kawar da duk fargaba saboda za a binne ta a makabarta ita ma idan ta mutu.
Bugu da kari don kawar da tsoronta, Abena ta ba da labarin yadda Michael ya gaya mata cewa wadanda suka mutu ba sa zama a makabarta domin da zarar an binne su, sai su fita can.

Exit mobile version