Mutane da dama na kamuwa da ciwon ‘Glacoma’ ba tare da sun sani ba, shi ya sa yake da mutukar muhimmanci da zarar mutum ya ji wani abu da ke nuna alamun ciwon ido, ya yi maza ya garzaya zuwa asibiti.
Har ila yau, ‘glacoma’ wata cuta ce wadda take kama idanu, ta sa ganin mutum ya samu matsala, wanda hakan kan jawo makanta. Kazalika wannan cuta, mafi yawancin lokaci ta fi kama masu shekaru, wadanda shekarunsu suka haura 40.
- Manoma 40,000 Za Su Amfana Da Takin Zamani Na Bunkasa Noman Rani A Filato
- Magance Bushewar Tafin Hannu A Lokacin Bazara
Sannan, idan akwai masu wannan cuta a gidanku ko a danginku, akwai barazana ko yiwuwar kamuwa da ita. Don haka, da zarar ka fara yawan jin kaikayi wanda ba ka saba ba ko ciwon ido, ka yi maza ka garzaya zuwa asibiti.
Haka zalika, masu fama da hawan jini da kuma wadanda suka jima suna shan sha-ka-fashe, su ma akwai barazana tare da yiwuwar kamuwa da wannan cuta a tare da su.
Haka nan, babu shakka gaske ne ba a warkewa daga wannan ciwo idan ya yi kamari ko ya ta’azzara, amma idan aka garzaya asibiti da wuri kafin ciwon ya gama yi wa mutum illa, za a iya taimaka masa wajen rage karfin ciwon ta hanyar ba shi magunguna, domin ka da mutum ya makance.
Har wa yau, yadda mutum zai san ya na da wannan ciwo na ‘glacoma’ shi ne, idan ya ga yana yawan yin ciwon ido ko ya ga ba ya gani sosai ko ya rika ganin hawaye na fita a idanuwansa ko kuma ya ga idanun nasa yana yin ja.
Shi yasa yana da kyau idan mutu ya ji idanunsa na yin ciwo, ya yi maza ya garzaya asibiti domin a duba a ga mene ne yake damun sa, dalili kuwa wani lokacin za a iyayin zaton ko ciwo ne da aka saba yi yau da kullum a ki zuwa asibitin, ba a san cewa wannan ciwo ba ne da ka iya haddasa makanta ko wani abu mai kama da haka, Allah ya kiyaye mu; amin.