Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai kawo muku kayataccen girkin Gasasshen nama mai dankali:
Ga dai irin abubuwan da uwargida za ta tanada:
Nama, Dankali, Albasa,Tumatur, kuri, Magi, Mai:
Ga kuma yadda uwargida za ki hada:
Da farko za ki soya dankali ki kwashe ki ajiye sannan ki yanka naman fale-fale kamar yankan dankalin sai ki dora kasko akan wuta ki zuba mai kadan idan ya yi zafi sai ki zuba naman nan a cikin kaskon ki zuba Magi da kayan kanshi, sai ki rage wutar ki rufe. Bayan dan wani lokaci sai ki juya bayan shi yadda ko ina zai gasu, sannan ki zuba albasa da tumatur da attaruhu akai wanda dama kin gyara su kin kuma jajjaga su idan suka yi laushi sai ki dora dankalin a kan gashashshen naman ki rufe bayan wani dan lokaci za ki ga duk kayan sun makale a jikin naman, shike nan kin kammala. A ci dadi lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp