An sake zaben tsohon shugaban Amurka Donald Trump a matsayin shugaban Kasar Amurka a zaben 2024, wanda ya yi nasara a kan mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris.
Wannan nasara ta Trump ta biyo bayan gagarumin zabe wanda ya kawo tsauri sosai tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma yankunan Amurka.
- Na Fi Jin Dadin Rubutu In Na Gaji Tibis – Maryam Faruk
- Sarkin Musulmi Ya Nemi A Daina Tsine Wa Shugabanni
Sakamakon zaben da aka gudanar ya nuna yadda Trump ya samu kuri’un da suka kai shi hanyar lashe zaben tare da samun rinjayen wakilan zabe na shugaban Kasa (Electoral College).
Wannan nasara ta kuma fito fili ne daga kuri’un wasu muhimman jihohin da aka sa ido sosai a kansu. Jim kadan bayan ayyana sakamakon, Trump ya gode wa magoya bayansa a wani jawabi da ya gabatar, yana mai cewa “Amurka ta ba mu wata babbar dama da ba a taba ganin irinta ba.”
Sakamakon wannan zabe zai ci gaba da jan hankali musamman ganin yadda ya kawo wani sabon shafi a tarihin siyasar Amurka, inda Trump zai zama daya daga cikin tsoffin shugabannin kasa da suka sake komawa kan mulki bayan shekaru hudu.
Wannan zabe na shekarar 2024 ya kuma janyo hankalin duniya saboda zai iya kawo sauye-sauye a manufofin Amurka a fannonin tattalin arziki da shige da fice da tsaro da kuma dangantakar Amurka da sauran kasashen waje.
Donald Trump ya samu kuri’u 279, yayin da ita kuma Kamala ta samu kuri’u 219.
Dama ana bukata ne dantakara ya samu kuri’u 270 na wakilan masu zabe domin lashe zaben na shugaban kasa.
Da fari a yammacin ranar Talata ne sakamakon zabe ya fara fitowa fili a zaben shugaban kasa tsakanin mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da tsohon shugaban kasar Donald Trump.
Dukkan ‘yan takarar biyu sun yi nasarar lashe zaben tun da wuri a wasu jihohi dake zaman tungarsu a zaben mai cike da tarihi da ka iya ganin Amurka ta zabi shugabar kasa mace ta farko.
Trump, wanda ke neman komawa fadar White House bayan ya sha kaye a shekarar 2020, ya kwace jiharsa ta Florida, inda ya samu wakilai 30 na jihar. Harris, kamar yadda aka zata, ya samu nasara a kananan jihohi masu yawa a Gabashin Amurka.
Dan takarar da zai lashe zaben na bukatar wakilai 270 daga cikin 538 domin ya samu nasara. Wanda ya yi nasara zai fara wa’adin shugaban kasa na shekaru hudu a watan Janairu.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi hasashen cewa kallo zai koma kan jihohi bakwai ne kacal a fagen siyasa, inda bincike ya nuna ‘yan takarar biyu na tafiya kankankan da juna – wanda hakan ya sa ake ganin mai rabo ne kawai zai samu.
A halin yanzu dai ya tabbata Tsohon Shugaban Kasar na Amurka shi ne ya yi nasarar lashe zaben na shekarar 2024, ya yi takwarorinsa na sauran kasashe ke ci gaba da aika masa sakon taya murna.