A halin yanzu, dakunan karatu (Libraries) ba su zama zallar cibiyar littafan karatu zalla ba; sun kasance masu rungumar fasaha da kuma sabbin hanyoyin da tafiya da zamani daidai da bukatun jama’a.
A zamanin nan na fasaha, dakunan karatu ba su tsaya zallar a zo cikinsu a zauna a dauki littafi a yi karatu kamar yadda aka saba a da can baya ba, yanzu cibiyoyin karatun da dama sun bi ayarin zamani wajen tafiya da zamani da kuma samar da littafai ta yanar gizo, shafukan yanar gizo domin bincike da sauran muhimman hanyoyi da zamani ya zo da su.
- CBN Ya Bayyana Sunayen Bankuna 41 Da Ya Aminta Da Ingancinsu A NijeriyaÂ
- Majalisar Dattawa Za Ta Kafa Dokar Kare Hakkin ‘Yan Aikatau A NijeriyaÂ
Bugu da kari, dakunan karatun sun kuma kasance cibiyoyin ba da dama ga jama’a domin samun hanyoyin mu’amala da fasahar zamani, tarukan bita, horaswa da kuma ba da dama domin bunkasa hanyoyin hadaka wajen kirkirar sabbin abubuwa ta hanyar zamani.
Ta hanyar runguma da amfani da fasaha, dakunan karatu na iya ci gaba da jan ragamarsu a bangaren ba da dama na yin karatu da taimaka wa jama’a wajen samun bayanai da bunkasa ilimin jama’a.
Wannan canjin ya bai wa dakunan karatu damar ci gaba da kasancewa wurare masu matukar amfani wajen koyon ilimi da fadada ilimi, bincike da saurin samun bayanai a tsakanin jama’a a fadin duniya. Saukin samar wa jama’a da hanyoyin shiga yanar gizo, littafai ta yanar gizo, littafai da ake sauraronsu ta sautin murya, mujallo sun kasance hanyoyin samun ilimi mafi sauki ga masu karatu a kowani lokaci a kuma ko’ina.
Wannan matakin ya kawo wani gagarumin sauyi ta bangaren ‘yancin samun bayanai. Masu amfani da dakunan karatu a yanzu suna da ‘yancin shiga a dama da su wajen koyon karatu da bincike ba tare da wani la’akari da nisan wuri ko kashe kudade ko samun tsangwama wajen neman ilimi ba.
Tafiya da zamani ya kai matakin da dakunan karatu sun iya samar da yanayi mai kyau da sauki da marmari ga masu amfani. A yayin da fasaha ke kara samun gurbin zama, su ma dakunan karatu za su ci gaba da rungumar hanyoyin da fasahan ya zo da su wajen ganin sun tabbatar da ilimi ya samu ga jama’a a zamanin da fasahar zamani ke bunkasa. Bincike ya gano cewa ta hanyar zamanin, dakunan karatu na samun damar saukaka wa jama’a da kuma rage kashe kudade wajen samun ilimi da bincike.
Sai dai kuma duk da wannan gagarumin ci gaba da ake fuskanta, a wasu yankunan ana kallon kamar akwai ‘yan matsalolin da muddin masu ruwa da tsaki ba su dauki matakan shawo kansu ba za a iya samun matsala.
Misali a Nijeriya wasu dakunan karatun na fama da matsalar rashin wadataccen kudin intanet (data) da jama’a za su rika amfani da shi wajen shiga yanar gizo domin bincike da karanta littafai ta yanar gizo. Kazalika, a wasu cibiyoyin akwai karancin na’urori masu kwakwalwa wanda hakan na gurgunta sa’ayin wasu matasa na neman ilimi da bincike.
Duk da yake mafi yawan dakunan karatu sun kasance cibiyoyin koyar da na’ura mai kwakwalwa, amma rashin wadataccen wutar lantarki na zama cikas ga cikan burikan wasu na samun ilimi cikin sauki da hanzari.