• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Asibitin Ƙauran Namoda Da Ya Inganta

by Leadership Hausa
1 year ago
gwamna

A ranar Talatar nan ne Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da babban asibitin Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, wanda aka yi masa gyara, tare da wadata shi da kayan aikin kula da lafiya.

Babban asibitin, yana kula da Ƙauran Namoda da maƙwabtanta, wanda kuma aka wadata shi da kayan aiki don ya samar da iingantacen kiwon lafiya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa babban asibitin, an samar masa da kayan aikin kula da lafiya, waɗanda suka haɗa da na’urorin binciken cututtuka, gadajen haihuwa, na’urar auna bugun zuciya (ECG), na’urorin binciken jini, babbar na’urar binciken jini ta ‘automatic hematology analyzer’, na’urar auna nauyi ta zamani, fitilar haskawa yayin aikin tiyata da dai wasu kayan kula da lafiya da daman gaske.

Sanarwar ta ƙara da cewa, asibitocin gaba ɗaya na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya, wanda ya kamata ya zama mai sauƙi ga al’ummar Jihar Zamfara.

A wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya nanata cewa babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai shi ne farfaɗo da taɓarɓarewar ababen more rayuwa da magance matsalolin da ke addabar dukkanin sassan tattalin arzikin jihar.

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

Matsalar Tasgadewar Kashin Baya

gwamna

“Wannan hangen nesa ya sa muka yanke shawarar samar da ajandar kawo sauyi da ta ƙunshi ginshiƙai shida, inda kiwon lafiya ya kasance ginshiƙi na uku, biyo bayan ilimi da tsaro.

“Manufarmu na farfaɗo da asibitoci shi ne mu tabbatar da cewa an samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’ar mu, walau a yankunan karkara ko a birane. Wannan fahimtar ta sa muka gyara tare inganta cibiyoyin kiwon lafiya da suka lalace, musamman a garuruwa masu muhimmanci irin su Kaura Namoda, da ke a tsakanin ƙananan hukumomi da kuma zama wuri mafi sauƙi ga yankunan da ke kewaye.

“Na yi farin cikin bayar da rahoton cewa, a cikin watanni 14 da suka gabata, mun samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari wajen gyara da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar nan.

gwamna

“Har ila yau, mun kammala shirye-shiryen ɗaukar ma’aikatan kiwon lafiya da horar da su, sayen magunguna da kayan aiki masu muhimmanci, da gabatar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara kyauta.

“Muna fatan waɗannan ayyukan za su haifar da ingantacciyar lafiya ga jama’armu ta hanyar rage mace-macen mata masu juna biyu, mace-macen jarirai, da daƙile cututtuka a faɗin jihar.

  • Badakalar Kudade: Kotun Daukaka Kara Ta Nemi Tsohon Gwamnan Kogi Ya Gurfanar Da Kansa A Kotu

 

“Bikin ƙaddamarwar na yau ya nuna aniyarmu ta samar da ingantaccen kiwon lafiya ga ɗaukacin mazauna Zamfara, ba tare da la’akari da wurinsu, matsayinsu ko kuɗin da suke samu ba.

“Tsarin aikin ya haɗa da sake gyara asibitin gaba ɗaya, tare da samar da tsayayyen wutar lantarki mai ƙarfin 32 kW, da sanya fitulun titi 25, da kuma samar da muhimman kayan aiki ga likitoci. Bayan kammala wannan ginin cikin nasara, ina da yaƙinin cewa mutanen Kaura Namoda da garuruwa da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su, yanzu za su samu damar cin moriyar kiwon lafiya mai sauƙi.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?
Kiwon Lafiya

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

October 5, 2025
Matsalar Tasgadewar Kashin Baya
Kiwon Lafiya

Matsalar Tasgadewar Kashin Baya

September 27, 2025
Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargaɗi Na Mako Ɗaya A Abuja
Kiwon Lafiya

Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargaɗi Na Mako Ɗaya A Abuja

September 8, 2025
Next Post
Tufka Da Warwarar Akidar Kwankwasiyya

An Kama Dan Uwan Kwankwaso Da Wasu 4 Kan Badakalar Magani A Kano

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.