Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa mutane 14 ne suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wasu motoci uku a Tashar Saleh da ke kan hanyar Bauchi-Toro zuwa Jos.
Ya ce hatsarin ya rutsa da motocin kasuwanci guda biyu da kuma wata motar gida.
Abdullahi ya ce motocin da abin ya shafa sun hada da Opel Vectra Saloon mai lamba: AA421KRF; Babbar tirela (DAF) mai lamba: GME 715XX da jar Mercedes Benz 190 mara lamba.
Ya ce, cikin Fasinjoji maza 15 da hatsarin ya rutsa da su, daya ne tak ya tsira babu rauni a tare da shi.
Ya ce, an kai wadanda suka samu raunuka zuwa babban asibitin Toro domin kula da lafiyarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp