Har kullum hukumomin kasar Sin na nacewa manufarsu ta sauke nauyin dake wuyansu, na wanzar da hadin gwiwa a fannoni daban daban, musamman karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC a takaice, da ma shawarar nan ta “Ziri daya da hanya daya” da sauransu, wadanda dukkaninsu ke tallafawa babbar manufar nan ta gina al’ummar bil adama mai makomar bai daya cikin hadin gwiwa.
Karkashin hakan ne ma, albarkacin ranar jami’an “Unguwar Zoma” ta kasa da kasa, tawagar jami’an kiwon lafiya ta kasar Sin ta 23 dake aiki a kasar Rwanda, da hadin gwiwar takwarorinsu na Rwanda, suka gudanar da bikin ranar “Unguwar Zoma” ta kasa da kasa, jiya Laraba 10 ga watan nan, a asibitin Masaka dake wajen birnin Kigali, fadar mulkin kasar.
Bikin dai ya samu halartar kwararrun jami’an kiwon lafiya, daga babban asibitin Baotou na jihar Mongoliya ta gida dake arewacin kasar Sin, wadanda suka halarce shi ta kafar talabijin, baya ga sauran sassan da suka yi hadin gwiwar shirya shi.
Ko shakka babu, irin wannan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya, muhimmiyar dama ce ta raya ci gaban fannin kiwon lafiya tsakanin kasashe masu tasowa.
Karkashin hakan, al’ummun kasashe masu tasowa na samun babbar gajiya daga kwararrun masana kiwon lafiya na Sin, kana takwarorinsu na kasashen Afirka, na kara samun kwarewa da sanin makamar aiki, da ma tallafin kayan kiwon lafiya daga bangaren kasar Sin, wadda ta jima tana tallafawa a wannan fanni.
Fatanmu shi ne irin wannan kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kawayenta na nahiyar Afirka zai dore, ya kuma ci gaba da haifar da fa’ida mai yawa ga sassan biyu a yanzu da ma nan gaba. (Saminu Hassan)