A kwanan nan Ministan Ma’adanai, Mista Dele Alake, ya bayyana alakar hakar ma’adanai da bisa ka’ida ba da ayyukan ta’addanci a kasar nan. A ta bakinsa, “Yawancin ayyukan ta’addanci da na ‘yan bindiga masu harkokin hakar ma’adanai ba bisa ka’idaba suke daukar nauyinsu a Nijeriya. Ba wai wadanda suke aikin hakar ainihin ma’adanan ba ne amma manyan masu kudi ne a sassan Nijeriya suke daukar nauyin ta’addancin”. A ra’ayinmu da muka wallafa a wani lokaci a baya mun yi irin wannan bayanin.
Mun sake dawo da sharhin ne don ya zama kalubale ga gwamnati domin ta samo hanyar warware matsalar. Dole ne a fallasa tare da kunyata wadannan mutanen. Minista Alake zai iya jagorantar wannan fafatawar.
- Jarin Waje Na Kai Tsaye Dake Shigowa Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 1.04 Cikin Watanni 11 Na Farkon Bana
- Gwamnan Zamfara Ya Gabatar Da Kasafin N432.5b Shekarar 2024
Al’amarin da ya shafi dangantakar ayyukan ta’addanci da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Nijeriya ya kara fitowa fili ne a wani rahoto da wata jaridar kasar Birtaniya ta ruwaito kan yadda ‘yan kasuwar kasar Sin suka mamaye harkar hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba kuma suke tallafa wa masu ayyukan ta’addanci a sassan Nijeriya. Jaridar ta kuma kara da cewa, ‘yan kasar Chanan suna cimma wannan buri nasu ne ta hanyar bayar da cin hanci ga wasu bangarori da al’ummar Nijeriya.
Amma kuma nan take ofishin jakadancin kasar Chana a Nijeriya ya karyata wannan zargin, tare da bayyana cewa babu cikakkun hujjoji na danganta kasar Chana da ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Yana da matukar muhimmaci a fahimci cewa, ba wannan ne karo na farko ba da ‘yan Nijeriya ke lura da cewa, ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba yana taimaka wa ayyukan ‘yan ta’adda a sassan Nijeriya. Wannan yana kara fitowa fili ne in aka lura da yadda ‘yan bindigar ke fuskantar jami’an tsaronmu da makamai na zamani masu karfi da kuma yadda suke yada farfaganda don dakile gaskiyar halin da ake ciki. A lokuta da dama wadannan ‘yan ta’addar suna tafka ayyukan ta’addanci ba tare da an hukunta su ba.
A matsayinmu na gidan jarida, mun yi imanin cewa, ba zai yiwu a ce, wadannan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba suna aikata ayyukan ta’addanci ba tare da an hukunta su ba, ya kamata hukumar da ke bayar da izinin hakar ma’adanai ta soke lasisin wadannan kamfanonin da ake zargi in ba haka ba to lallai dole ministan ma’adanai ya fito fili ya yi bayani mai gamsarwa a kan lamarin.
Tun da farko mun kafa ayar tambaya a kan yadda hamshakan masu kudi ke tafiyar da harkar hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, amma kuma idan har akwai hannun wasu kasashen waje a ayuyykan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba to mun san hakan ba zai taba yiwuwa ba sai an samu hadin kan ‘yan Nijeriya.
Yana da matukar muhimmnanci a fahimmci cewa, Nijeriya na da mutane da kowacce al’umma ke mutuntawa suna kuma daukar su da matukar muhimmanci, irin wadannan mutane ne suke daukar nauyin shigowar ‘yan kasashen waje ta hanyar samar musu da Biza da sauran ka’idojin da suke bukatar cikawa, in ma sun samu matsala su ne dai ke tabbatar da ba a hukunta su ba a lokuta da dama. Wannan ne yake kara bayyana mana ainihin dalilin da ya sa suka samu hanyar shigowa cikin kasa tun da farko.
Harkar hakar ma’adanai ba wata abu ba ne da za a iya yi a boye, abu ce da ke bukatar manyan kayan aiki da ma’aikata na cikin gida da kasashen waje yana kuma bukatar zuba jari mai yawan gaske. Ana kuma fitar da abin da aka samu ta hanyoyin shiga da fita kasar nan (ta kasa, ruwa da ta sama). Akwai kuma jami’ai da hukumomin da aka dora wa alhakin kula da wadanna kafofi, shin suna sane da ayyuykan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ko kuma suna yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne?
In har ta hanyar ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba Nijeriya na asarar kudaden shiga to mene ne jami’an tsaronmu da sauran hukumomin gwamnati ke yi don dakile ayyukan masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa?
A ra’ayinmmu, babu wani aiki na masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a halin yanzu sai da kawai tare da ayyukan wasu tsageru da suke amfani da tabarbarewar harkoki a kasa na abin da ya shafi cin hanci da rashin iya gudanar da aiki a ma’aikatun gwamnnati don cutar da tattalin arzikin kasa, suna daukar nauyin ‘yan ta’adda don su dauke hankali daga ainihin abin da ke faruwa a yankunan kasar nan inda wasu ‘yan kalilan ke tatsar dukiyoyin kasa.
A duk lokacin da aka samu hannun kasashen waje a harkokin hakar ma’adanai dole a fuskanci matsalolin tsaro, muna da darussa daga abin da ya faru a kasashe irin su Saliyo da Kongo. Duk da cewa, majalisar dinkin duniya na da hanyoyin da take fuskantar irin wadannan matsalolin. Ya kamata kafin tarayyar kasashen duniya su kawo mana dauki dole gwamnatin Nijeriya ta amince da cewa, lallai akwai matsala a bangaren hakar ma’adanai a kasar nan, ta kuma dauki matakin da suka dace don magance yadda masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ke cin karensu babu babbaka, dole gwamnati ta toshe duk wata kafa kafin a kai ga dora wani laifi a kan wani. Ya kamata gwamnati ta dauki kudurin fuskantar lamarin kai tsaye ba tare da nuna tsoro ba.