Abubakar Abba" />

Yadda Haraji Barkatai Da Ayyukan Makiyaya Suka Jefa Noma Da Kasuwanci Tsaka Mai Wuya

Jigajigan masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma da kuma tattalin arzikin kasar nan sun koka kan yadda gwamati ke yawan karbar haraji barkatai kan amfanin gona, inda suka yi nuni da cewa, hakan ya sa gwamnatocin ke kashe fannin aikin noma a kasar

Sun kuma ankarar da gwamnatin cewa, in ba a mayar da hankali ba kasuwancin na amfanin gona nan ba da dade wa ba zai durkushe.
A cikin sanarwar da mai magana da yawunsu, Alhaji Bala Abdulkadir ya raba wa manema labarai sun ci gaba da cewa, za a iya funkantar karancin abinci a kasar nan saboda ayyukan ce, za masu kai hare-hare kan manoma a wasu sassan kasar, rikicin manoma da makiyaya, inda kuma hakan zai tilasta wa manoman barin sana’ar ta noma.
Alhaji Bala Abdulkadir ya ci gaba da cewa, bugu da kari, karbar harajin barkatai da wasu gwambatocin jihohi a kasar nan suka kirkiro da su, hakan bai taimaka wa manoman, inda ya kara da da cewa. Kowa ya san aikin noma na da matukar wuya
A cewar Alhaji Bala Abdulkadir, akasarin kasashen da aka ci gaba, Gwamnatocin su, na samar wa da manoma sauki kan karbar haraji, inda kuma wasu ke kebe manoma daga biyan haraji, musamman domin su wadata kasashen su da abinci mai dimbin yawa.
Sai dai, Alhaji Bala Abdulkadir ya yi nuni da da cewa, wasu daga cikin kalubalen da fannin na aikin noma ke fuskanta sun hada da, rashin samun yanayi mai kyau, karancin ruwan sama, farin dango, barkewar annobar cututtuka ga dabbobi da sauransu.
Alhaji Bala Abdulkadir ya yi nuni da cewa, amma ya na da kyau a bayyana cewa a yanzu, tsdar man Dizil da tsadar wutar lantarki, su na zamo wa fannin barazana, inda hakan ya ke kara zamo wa nauyin kan manoma.
Ya ci gaba da cewa, wadannan hujjojin da na zayyano su ne manyan dalilan da suka sa, kasuwancin noma ba zai iya jure wa yawan karbar haraji ba, inda ya ci gaba da cewa, kasuwancin noma ba zai dore ba, in been saboda sabbin karbar haraji da gwamnatocin jihohin suka kirkiro da su.
Alhaji Bala Abdulkadir ya yi nuni da cewa, harajin yakamata ne a karba kan ribar da manoma suka samu, amma a yanzu, abin ba haka ya ke ba ganin cewa gwamnati na kokarin tilasta wa kan karbar haraji daga kudaden manoma da kuma a kan kudaden da suka ranto domin yin noma, inda ya kara da cewa, a baya, manoma na biyan haraji ne ga Hukumar tara Haraji ta Tarayya (FIRS), haka kuma jihohi na karbar haraji daga gun daraktocin kamfanoni da wanda ake karba daga gun ma’aikata sai kuma harajin kudin karatu.
Alhaji Bala Abdulkadir ya yi da cewa, gwamnati ta kuma kirkiro da wasu karbar haraji da ban da ban, inda hakan ya kara wani sabon nauyi kan manoma.
Ya zayyano sauran harjin da ake karba kan manoman don riba da suka hada da, harajin muhalli da kuma haraji kan dagwalon da ke fita daga masana’antun sarrafa amfanin gona, cajin kudi kan mallakar filin noma da Ma’aikatar Aikin Noma da Raya Karkara ta ke karba, kirkiro da karbar haraji kan amfanin gona da kuma amfanin da manoma suka sarrafa, wadand suka hada da, cajin da ake karba kan kwon ‘yan tsaki da abincinsu da sauransu.
Alhaji Bala Abdulkadir ya kuma zargi Ma’aikatar Sufuri, na da masu gudanar mata da aiki da dama, da suke cin zarafin manoma yayin da suka yo jigilar amfanin ginakansu a hanya, inda ya bayyana cewa, haka jami’an tsaro kamar ‘yan sanda na b.I.O, ‘yan sanda masu bayar da hannu a kan tituna, jami’an kiyaye huddura FRSC, masu karbar haraji na kananan hukumomi, su na karbar haraji barkatai daga gun manoman, inda ya kara da cewa, abinda ya fi muni shi ne, irin harajin da wadanda gwamnatocin suka dauka kan kwangila domin su tara masu harajin.
A cewar Alhaji Bala Abdulkadir, su na tara harajin miloyoyin naira, yakamata gwamnati ta Sani cewa, suma manoman ‘yan kwadago ne kuma karbar haraji barkatai daga gun manoman kamar ana son a kore su daga cikin sana’ar ce, inda kuma hakan zai kara janyo rashin aikin yi, kara janyo rashin tsaro da kuma haifar da yunwa a kasar nan.
Alhaji Bala Abdulkadir ya yi nuni da cewa, lokaci ya yi da daukacin matakan gwamnati uku na kasar nan za su kare manoma daga biyan haraji barkatai da kuma rage masu kalubalen da suke fuakanta a fannin, inda ya kara da cewa, ya zama wajibi a cire manoman daga biyan haraji a kasar nan.

Exit mobile version