Kwanakin baya ne kamfanin jaridar ‘Daily Champion’ ya karrama shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa Nijeriya (NPA), Mohammed Bello-Koko, da kambun jagora kuma shugaba a bangaren harkar safara da mu’amala da tashohin jiragen ruwan Nijeriya na shekarar 2022.
Wannan karramawar na zuwa ne saboda jajircewarsa a wajen bunkasa harkokin gudanarwa na tashoshin jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) musamman tashoshin da ke can cikin teku, da kuma yadda aka samu karin kudaden shiga da hukumar ke zubawa a asusun gwamnatin tarayya, wani abin da aka dade ba a samu irinsa ba, haka kuma ya yi kokari a wajen samar da sabbin kayan aiki a tashoshin ruwan Nijeriya wadanda suka yi daidai da yadda ake samu a kasashen duniya, wanda hakan ya taimaka wajen daga darajar Nijeriya a kasashen duniya.
Wasu dalilai da jaridar ta ‘Daily Champion’ ta bayyan a matsayin abin da suka sa hukumar gudanarwar jaridar ta karrama Mohammed Bello Koko sun hada da yadda ya samar da wani tsari ha musanmman da ake kira da ‘Port Community System (PCS)’ wanda haka ya taimaka wajen samar da tsari guda daya na gudanar da harkokin tashoshin ruwa ta yadda aka yi maganin maimaita aiki wanda a baya sune ke haifar da bata lokaci da jinkiri wajen sallamar abokan huldar, masana sun kuma yaba da wannan kokarin don ya taimaka wajen mayar hankali ga tashoshin jiragen ruwa dake a yankunan kudancin kasar nan.
Hukumar gudanarwar kamfanin jaridar ‘Daily Champion’ ta bayyana cewa, ta karramar Bello-Koko ne saboda yadda ya samar da sabbin tsare-tsare a harkokin gudanarwar hkumar NPA wanda hakan ya matukar taimakwa wajen bunkasa hulumar a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki, zamantaewwa da jindadin ma’aikata, musamman kuma yadda aka samu karin kudaden shiga ga kasar mu Nijeriya.
Hukumar gudanarwar jaridar Daily Champion sun kwatanta Mohammed Bello Koko da wani gogagge da ya yi fice a wajen gudanar da hukumar NPA ya kuma yi fintinkau a wajen tsimin kudaden hukumar, an kuma kwatantan shi da mutum wanda ya kama kansa ya rike mutuncinsa a rayuwarsa na yau da kulum da kuma yanayin aikinsa na gwamnati.
Shugaban kamfanin na jaridar Daily Champion, Dakta Nwadiuto Iheakanwa, ya bayyana cewa, irin jajircewar shugaban NPA Bello Koko da yadda yake gudanar da shugabancin hukumar ya taimaka wajen bunkasa harkokin tashoshin ruwan Nijeriya ya kuma daga darajar NPA a idon duniya fiye da yadda ake tunani, musamman abin da ba a taba gani ba a ‘yan shekarun nan.
Ya kuma kara da cewa, ayyukan alhairin da Mohammed Bello Koko ya yi sun hada da samar da sabbin gine-ginen ofishoshin ma’aikata da tabbatar da biyan hakokin ma’aikata wanda da wahala a samu wata hukumar gwamnati da take da matsayi irin wannan.