Masana fannin noma a Nijeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakin su kan yadda, fannin ya samu koma-baya saboda karancin takin zamani da tsadarsa a daminar bana.
Har ila yau, sun yi nuni da cewa, karancin da kuma tsadar ta takin, zai haifar gibi a fannin da kuma shafar tattalin arzikin Nijeriya.
- Kudin Da NNPC Ke Kashewa A Tallafin Mai Ya Wuce Kima – Hamid Ali
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
Kuma wadannan matsalolin, a cewar kwararru na janyo gibi ga irin amfanin gonar da manoman ke samarwa.
A cewarsu, a wasu shekarun baya, mahukunta a kasar sun samar da takin wadatacece kuma a cikin rahusa, amma a yanzu takin ya zama Gwal.
Sun kara da cewa, matsalar ta fi shafar manoman da ke yin noma a karkara, inda samun takin ke ci gaba da kara zamar masu babbar matsala.
“A wasu shekarun baya, mahukunta a kasar sun samar da takin wadatacece kuma a cikin sauki, amma a yanzu takin ya zama Gwal”.
Sun bayyan cewa, cin hanci da rashawa a tsarin na samar da takin, na daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta na samar da wadataccen sa a kasar.
Duk da cewa, mahukunta a matakan gwamantin uku na kasar sun shelanta cewa, sun samar da takin a cin farashi mai sauki, amma manoman ba su gani a kasa ba, musaman ganin yadda tsadar ta sa musamman ta hana manoman kasar musamman kanana iya sayen takin don noma gonakan su.
“Matsalar ta fi shafar manoman da ke yin noma a karkara, inda samun takin ke ci gaba da kara zamar masu babbar matsala”.
“Shelanta cewa, sun samar da takin a cin farashi mai sauki, akasari idan aka bincika, magana ce kawai ta siyasa, amma ba a zahiri ba”.
Sun sanar da cewa, abin takaici yadda wasu `yan siyasa a kasar ke yin yakin neman zabe da takin don a zabe su, wanda da zaben ya wuce, takin zai kara yiwa manoman nisa.
Masanan sun kuma koka kan tasirin samar da takin, inda suka bayyana cewa, za fara damina a watan hudu, amma ba za a samun takin a kan lokaci, inda hakan ke sanya wa manoman ke fara yin noman a kan kurarren lokaci.
Har ila yau, sun sanar da cewa, ya zama wajibi mahukunta a fannin na samar da takin a kasar nan, su dinga baiwa manoman kasar, musamman kanana tallfi don su kara habaka sana’ar ta su ta noma da kuma samar wa da kansu da kudin shiga.