Ga duk mai bibiyar alkaluman bunkasar tattalin arziki na Sin da kasashen Afirka, ya kwana da sanin yadda a gwamman shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya, da zuba jari ta kasashen nahiyar Afirka, inda ya zuwa shekarar 2021 da ta gabata, darajar hada hadar cinikayya tsakanin sassan biyu ta kai dalar Amurka biliyan 254, adadin da ya dara wanda ke tsakanin kasashen Afirka da kasar Amurka.
Kazalika, tuni kasar Sin ta zamo babbar mai zuba jarin kai tsaye a kasashen Afirka, matakin da ya tallafa matuka wajen samar da dubban guraben ayukan yi a kasashen nahiyar, wanda kuma ya ninka jarin kai tsaye na waje da Amurka ke zuwaba a Afirka.
Hakan ne ma ya sa a baya bayan nan, babbar sakatariyar taron cinikayya da samar da ci gaba ta MDD ko UNCTAD Rebeca Grynspan, ta jinjinawa gudummawar da Sin ke bayarwa, wajen habaka cinikayya, da zuba jari a Afirka. Tana mai bayyana Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar tafiya ta al’ummun kasa da kasa.
Ko shakka babu, kasar Sin ta riga ta zama muhimmiyar abokiyar cinikayya, da cudanya a fannoni daban daban tare da kasashen Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa, bisa fifiko da take da shi na ci gaba, cikin gwamman shekarun da suka gabata.
Mun san cewa, hada-hadar cinikayya tsakanin kasashen duniya muhimmin jigo ne na bunkasa tattalin arzikin kasashe, musamman ma ga kanana da matsakaitan kasashe, saboda rawar da hakan ke takawa, wajen samar da guraben ayyukan yi da bunkasa kudaden shigar jama’a.
Don haka a jimlace, muna iya cewa, Sin ta taimakawa kasashen nahiyar Afirka, da damammakin fadada cinikayyarsu a matakin kasa da kasa, a muhimman fasahohi na samar da hajoji, da sarrafa kayayyakin masana’antu, da hada-hadar shige da ficen amfanin gona da dai sauransu. (Saminu Hassan)