Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Yadda Kasuwannin Sayayya Suka Samu Tagomashi Sosai A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin Ya Nuna Karfin Tattalin Arzikinta

by Sulaiman Ibrahim
February 18, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
3 min read
Yadda Kasuwannin Sayayya Suka Samu Tagomashi Sosai A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin Ya Nuna Karfin Tattalin Arzikinta
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

A lokacin hutun murnar bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a bana, mutanen da suka yi murnar biki a inda suke aiki sun ji dadin bikin ta mabambantan hanyoyi. Alal misali, yin sayayya da murnar bikin ta yanar gizo, da samun hidima a gida, da yawon shakatawa a wuraren da ke bayan gari da dai sauransu. Kasuwannin sayayya sun samu tagomshi sosai a bana.
A lokacin hutun murnar bikin Bazara a bana, an nuna fina-finai da dama, wadanda suka kara azama kan kasuwannin fina-finai. Darektocin gidajen sinima a sassa daban-daban na kasar Sin sun yi bayani kan cinikinsu a bana kamar haka.


“Yawancin masu kallon fina-finai a nan matasa ne, kana kuma iyalai da yawa sun zo kallon fina-finai.”
“A ‘yan kwanaki 5 da suka wuce, a ko wace rana an nuna fina-finai sau 13 ko 14, yayin da yawan kudin tikiti ya kai kudin Sin RMB yuan dubu 200. Lamarin da ya wuce zatonmu.”
“Muna kusan sayar da dukkan tikiti a ko wace rana.”
Alkaluman da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta gabatar a yammacin ranar 17 ga wata sun nuna cewa, jimilar kudin tikitin kallon fina-finai da aka samu a wannan lokacin hutun murnar bikin Bazara ta wuce yuan biliyan 7.5 baki daya, adadin da ya karya matsayin bajimta a tarihi bisa makamancin lokaci na ‘yan shekarun baya. Jimilar kudin tikitin kallon sinima da aka samu a cikin kwanakin 45 na farkon bana ya wuce yuan biliyan 10, adadin da ya kai rabin jimilar kudin tikitin shekarar bara baki daya.
Yadda kasuwannin fina-finai suka samun ci gaba sosai ya nuna karfin kasar Sin ta fuskar kasuwannin sayayya a lokacin hutun murnar bikin Bazara a bana.
Ban da haka kuma, mutane sun yi sayayya ta sabbin hanyoyi a kasar Sin a bana.
Alkaluma sun shaida cewa, a lokacin hutu na murnar sabuwar shekara a bana, jimilar kudin da aka samu daga yin sayayya da cin abinci a dakin cin abinci a duk fadin kasar Sin ta kai yuan biliyan 821. Sa’an nan kuma jimilar kudin da aka samu daga bangaren yin sayayya kan yanar gizo a kwanaki 6 na farkon sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta zarce yuan bililyan 120, yayin da yawan kunshe-kunshen da kamfanonin kai kaya na kasar Sin suka karba ya kai miliyan 480, wanda ya ninka na makamancin lokaci na bara har sau 3.
An sayar da abubuwan murnar sabuwar shekara, kayayyakin lantarki na gida da sauran kayayyakin gida, da kayayyakin motsa jiki da dai sauransu masu tarin yawa a kasar Sin a kwanakin baya, a ciki kuma karuwar kayayyakin da suka hada da lu’ulu’u, da tufafi, da takalma, da hula, da kayayyakin kwalliya da aka sayar ta wuce kaso 100. Bayan haka kuma, yawan danyen furanni, da shuke-shuke, da kayayyakin ado na zinariya da aka sayar ya karu kwarai da gaske.
Har ila yau, jimilar kudin da aka kashe a dakin cin abinci a wannan lokacin hutu na murnar sabuwar shekara ta karu da kaso 1.3 bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Har ma jimilar kudin da aka kashe wajen sayen abinci kan yanar gizo ta karu fiye da sau 2.
Gudanar da bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a inda ake aiki ya kara azama kan yawon shakatawa a inda ake aiki, da wurare makwabta, da kuma ta hanyar tukin mota da kai. Wuraren shan iska, da dakunan ajiye kayayyakin tarihi, da filayen wasan kankara da sauran wuraren nishadantarwa, sun karbi mutane masu yawan gaske. Mutane da yawa sun yi odar dakuna a otel-otel a wuraren da ke bayan gari.
Yadda kasuwannin sayayya suka ci sosai a lokacin hutun murnar bikin Bazara ya nuna kyan karfin tattalin arzikin kasar Sin. Gu Xueming, shugaban kwalejin nazarin hadin kai ta fuskar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasa da kasa na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, “Kasar Sin ta fara da kafar dama a bangaren kasuwannin sayayya a bikin Bazara, wanda ya shaida cewa, kasar za ta iya ci gaba da kara azama kan habaka harkokin sayayya da bukatu a cikin gida. Babbar kasuwa a gida da kuma kyautatuwar tsarin sayayya, za su taimaka mata raya tattalin arziki.”(Tasallah Yuan)

SendShareTweetShare
Previous Post

Yawan Kudin Da Sinawa Suka Kashe A Yayin Hutun Bikin Bazara Ya Shaida Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar

Next Post

Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Sansanin Jami’ai Na Iyakar Kasa A Akwa Ibom

RelatedPosts

Sabon Nau’in Rigakafin Cutar COVID-19 Da Sin Ta Samar Zai Taimaka Wajen Yakar Cutar

Sabon Nau’in Rigakafin Cutar COVID-19 Da Sin Ta Samar Zai Taimaka Wajen Yakar Cutar

by Sulaiman Ibrahim
6 hours ago
0

Daga CRI Hausa Shugaban cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka...

Yadda Shugaba Xi Jinping Yake Ba Da Jagoranci Ga Aikin Kula Da Lardin Qinghai

Yadda Shugaba Xi Jinping Yake Ba Da Jagoranci Ga Aikin Kula Da Lardin Qinghai

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga CRI Hausa A jiya Lahadi, shugaba Xi Jinping na...

Shaidu Sun Karyata Jita-Jitar Da Ake Yadawa Game Da Alluran Riga-Kafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin

Shaidu Sun Karyata Jita-Jitar Da Ake Yadawa Game Da Alluran Riga-Kafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga CRI Hausa Jiya Lahadi, mamban majalisar gudanarwa kana ministan...

Next Post
Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Sansanin Jami’ai Na Iyakar Kasa A Akwa Ibom

Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Sansanin Jami’ai Na Iyakar Kasa A Akwa Ibom

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version