Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home KIWON LAFIYA

Yadda Maganin Hawan jini Ya Fi Amfani Lokacin Barci – Rahoto

by Muhammad
March 23, 2021
in KIWON LAFIYA
2 min read
Barci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Don a tabbatar da an samu nasarar amfani da maganin cutar hawan jini, a yi kokari a kiyaye da shan maganin kafin akai ga yin barci. Wannan wata hanya ce mai sauki da za a iya kubutar da rayuwa, kamar yadda mujallar ‘European Heart’ ta ruwaito.

Wasu magungunan suna bayar da kariya ne daga faruwar bugun zuciya da kuma shanyewar bangaren jiki, idan aka sha su da dare kafin a kwanta barci, maimakon da safe kamar yadda bincike ya nuna wasu na yin hakan.

Masana sun tabbatar da cewar, jikin dan Adam kamar agogo ne dake da lokuta na musamman, da ya fi bukatar karbar magani.

 

Samar da lokacin da ya dace don bai wa jiki magani:

Akwai kwararan shaidu da suka nuna cewa, magunguna da dama da suka hada da na ciwon zuciya sun fi amfani a wasu kebabbun lokuta.

Gwajin da aka yi, wanda kuma ba a dade yi ba kuma mafi girma da aka taba gudanarwa kan cutar hawan jini, da ya hada da masu shan maganin cutar 19,000 a kasar Sipaniya, da farko an kasa masu shan maganin ciwon hawan jini gida biyu.

Kashi na farko sun sha maganin ne da safe yayin da kuma shi kashi na biyu suka sha da dare kafin su kwanta barci.

Masu gwajin sun rika bin diddikin abubuwan da suke faruwa har tsawon kwanaki biyar ko kuma fiye da hakan.

Kashi na biyu kuma da suka sha maganin a lokacin da za su kwanta barci, sun kauce wa samun bugun zuciya da ya kai ga sanadiyar mutuwa ko shayewar barin jiki da kashi hamsin cikin dari.

Duk kuwa da yake ita cutar hawan jini wani ciwo ne da take lafawa da dare, lokacin da dan adam yake hutawa ko kuma ya ke yin barci.

Idan har irin wannan lokaci bai sa cutar ta sauka ba, to kuwa ta yi tsanani sosai kenan, da za ta iya haifar da bugun zuciya ko shanyewar jiki ga mai ita, ko da wanne lokaci kamar yadda masana su ka gano bayan da suka gudanar da bincike.

Bugu da kari kuma binciken ya bayyana cewa shan magani da yamma ko kuma lokacin barci, yana sa a iya gane yadda matakin hawan jinin mutum ya ke, musamman ma ga wadanda ke fama da cutar.

Duk da yake babu wani tsari da aka fitar don shan maganin cutar hawan jini, kuma likitoci sun fi ba da shawarar shan maganin cutar da safe, da nufin saukar jini da safe wanda kuma wani dalili ne, da ba ingantacce ba.

Banessa Smith ta gidauniyar kula da zuciya ta British Heart Foundation, ta ba da shawarar cewa idan mutum yana amfani da maganin cutar hawan jini, yana da kyau ya tuntubi likita kafin ya canza lokacin da ya ke shan magani, duk da fahimtar tasirin da zabar lokacin shan magani ya ke da shi.

Ta kara da cewa akwai dalilai da ya sa likitocin suke zabar wa marar lafiya lokacin da zai sha magani.

Yanayin tsarin rayuwa shi ma ya kan yi tasiri kan cutar hawan jini.

A kan haka ne masana suke kira da a guji wasu abubuwa kamar haka:

Shan giya

Shan tabar sigari

Kiba

Rashin motsa jiki

Yawan cin abincin da yake gishiri sosai.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ba A Taba Dan Wasa Kamar Ronaldo Ba A Duniya – Juventus

Next Post

Za A Yi Wa Kanawa Rigakafin Korona A Zababbun Asibitoci 509 – Gwamnati

RelatedPosts

Lassa

Yadda Zazzabin Lassa Ya Lakume Rayuka 176 A Nijeriya

by Muhammad
3 days ago
0

Daga Abubakar Abba, Hukumar dakile  yaduwar cututtuka ta kasa NCDC...

Uku Daga Cikin Cututtukan Kansa Da Suka Fi Hadari

Uku Daga Cikin Cututtukan Kansa Da Suka Fi Hadari

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Masana harkokin lafiya sun yi tabbacin...

Marmari

Kayan Marmari 12 Da Ake Bukatar Yawaita Sha Lokacin Zafi

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Sau da yawa kuma in ji...

Next Post
Asibitoci

Za A Yi Wa Kanawa Rigakafin Korona A Zababbun Asibitoci 509 – Gwamnati

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version