Umar A Hunkuyi" />

Yadda Masu Kamuwa Da Cutar Kwarona Ke Warkewa A Nijeriya – NCDC

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa (NCDC), ta yi magana a kan yanda masu fama da cutar nan ta Kwarona suke samun sauki a cikin kasar nan.

Babban daraktan hukumar ta NCDC, Chikwe Ihekweazu,  ya bayyana cewa kashi 90 na masu fama da cutar ta Kwarona duk sun samu sauki ba tare da sun yi amfani da wani magani na musamman ba.

Ya yi nuni a ranar Laraba da cewa, wanda ya kamu da cutar ta Kwarona a bisa ka’ida yana da bukatar abin da zai taimaka wa jikinsa ya farfado da kansa, kamar yanda ya yi ishara ga Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde, a matsayin misali.

“Ya kamata mu gane cewa kashi 90 na wadannan marasa lafiyar na Kwarona duk sun warke ne ba tare da an yi masu wani magani ba. Don haka in har ka yi amfani da wani abin, sannan ka ce abu kaza da na yi amfani da shi ne ya sabbaba mani samun saukin, wannan ya rage naka ne.”

“Cutuka irin wadannan, kadan daga cikinsu ne suke da magani. Ka je Asibiti a sabili da kamuwa da cutar COBID-19, sai aka sanya maka na’urar da za ta taimaka maka yin numfashi. Tabbas wannan na’urar ba ita ce maganin ba; an dai sanya maka ne domin ta taimaka maka wajen tsawaita rayuwarka har zuwa lokacin da za ka sami sauki,” in ji shi.

Ya zuwa ranar Laraba da yamma, hukumar ta NCDC ta tabbatar da karin mutane 22 da suka kamu da cutar, 15 daga cikinsu duk daga Jihar Legos ne, hudu kuma daga babban birnin tarayya Abuja, biyu daga Bauci da kuma mutum guda daga Jihar Edo.

Hakan kuma shi ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a Nijeriya zuwa 276 a yammacin ranar ta Laraba, inda 44 daga cikinsu suka warke daga cutar, shida kuma cikinsu suka mutu.

 

Exit mobile version