Sama da matasa ‘yan Nijeriya miliyan biyu ne suka kasance ‘yan zaman kashe-wando tun bayan dakatar da saidawa da rijistar layukan waya da gwamnatin Nijeriya ta yi ta hannun hukumar sadarwa.
Kungiyar dillalan layuka ta (ATOASDA) ita ce ta shaida hakan a ganawarta da ‘yan jarida a Kaduna.
Dilolin layukan wadanda suka ce suna sane da kokarin gwamanti na yunkurin dakile matsalar tsaro da ake samu ta hanyar amfani da layukan sadarwa wanda suka kuduri aniyar hada bayanan layuka da lambar shaidar kasancewa dan kasa (NIN), amma kuma hakan ya jawo wa matasa sama da miliyan biyu kasancewa marasa aikin yi wanda hakan ma wani karin barazana ne.
Shugaban kungiyar ATOASDA na kasa, Hassan Yakubu ya yi bayanin cewa kungiyar tana da cikakken rijista da hukumar kula da kamfanoni ta kasa (CAC) wadanda mambobinsu suka kasance jami’an da ke taimaka kokarin gwamnatin tarayya na kare rayuka da dukiyar jama’a.
Ya ce, mafiya yawan wakilan saida layuka da sarrafa su sun kasance ne ‘yan shekaru 20 zuwa 40 da suke aikin rijista wa jama’a da kuma sabunta musu layukansu da aka dauka aikin hakan, wanda ya ce yanzu duk sun kasance kawai ‘yan zaman kashe wando.
Ya ce, suna lale da dukkanin wani tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati na tabbatar da tsaftace harkokin sadarwa, don haka ne ma suka yi fatan a samu nasarar kammala aikin hade lambobin bayanan layuka da na shaidar kasancewa dan kasa cikin kwanciyar hankali domin bada damar cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Daga nan sun roki a bada damar a ci gaba da saida layuka da rijistar sabbi ko tsoffi domin jama’a su cigaba da samun aikin dogaro da kai a daukacin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan.