Wani matashi mai suna Sunusi Ali Musa mai kimanin shekara 30, ya fara sha’awar koyon kira ne lokacin da yake da shekara 10, musaman kasancewar mahaifinsa injiniya ne a fannin kayan aikin noma, musaman wajen gyaran tantan.
Matashin ya samu shaidar kammala karatu a fannin yin walda a Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano.
Ya kuma mayar da hankali ne wajen kera injin kyankyashe kwan jimina ta hanyar yin amfani da inji mai aiki da hasken rana.
- Bai Wa Hukumomin Alhazai Na Jihohi ‘Yanci Zai Taimaka Wajen Inganta Aikin Hajji – Barista Abdullahi
- An Nemi Fulani Su Manta Da Bambancin Da Ke Tsakaninsu Don Kubuta Daga Matsalar Tsaro
Matashin yana kera injin ne a gidansu da ke rukunin gidaje na unguwar Shagari a jihar Kano, inda yake da ma’aikatan da ke taya shi wannan aikin.
“Na mayar da hankali ne wajen kera injin kyankyashe jima ta hanyar amfani da inji mai aiki da hasken rana”.
Ya kuma kara samun karfin kwiwar yin wannan injin ne, ta hanyar karo ilimi daga kwararru a fannin kira.
Baya ga kera injin kyankyasar kwan jimina, yana kuma kyankyashe kwan sauran.
Ya ce, ya fara yin kyankyasar ce da kwan tsuntsaye da kuma na Kajin gidan gona ta hanyar gargajiya, bayan bukatar kyankyasar ta karu ne ya farayin kirar injin na kyankyasar kwan jimina, wanda zai iya kyankyashe a kalla kwai 50.000.
“Na kara samun wani ilimi ne ta hanyar kwararru a fannin yin kira”.
A cewarsa, ya kyankyashe daruruwan kwan jimina, inda a yanzu yake sayar da kwan daga naira 200,000 zuwa naira 250,000, amma idan zai yi mutane kyankyasar kwayayen suna biyan naira 5,000 a kan kowanne kwai daya.