Al’ummomin wasu kauyuka na yankin Bwari, daya daga cikin kananan hukumonin babban birnin tarrayar Nijeriya, Abuja, na cikin zaman dar-dar game da kamarin da suke cewa matsalar tsaro ta yi a yankin.
A makon da ya gabata rahotanni sun ce mutum bakwai ne ‘yan gida daya, wasu ‘yan bindiga su ka yi awon gaba da su, tare da neman kudin fansa kafin su sako su.
- Asalin Abin Da Ya Faru Game Da Dawowar ‘Yan Bindiga Hanyar Kaduna Zuwa Abuja – ‘Yansanda
- Bankin Duniya Ya Yi Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 3.3 A 2024
Wannan fargaba da ake fama da ita a wannan yankin ta shafi garuruwa da dama da ke kewaye da karamar hukumar.
Wata mazauniyar yankin da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa lamarin rashin tsaron da suke fuskanta ya jawo ba sa iya gudanar da harkokin rayuwarsu cikin natsuwa saboda tsoron hare-haren ‘yan bindiga da suke yi.
‘Bwari, gaskiya babu sauki yanzu fa, cikin kwanakin nan ana cikin tashin hankali domin ana bin gidajen mutane da ke unguwanni daban-daban na yankin ana kwashe su”, in ji ta.
Ta kara da cewa mazauna yankin ba su da wata masaniya kan wadanda ke aikata wannan mummunan aiki, sun dai san cewa akasari su kan yi garkuwa da mutane ne domin neman kudin fansa.
Ta ce ‘sai su kira wani kudin da watakila har mutum ya mutu ba zai taba ganinsu ba. Sai a kama talakan da ba shi da abincin ci, a ce wai ya kawo miliyan hamsin, a ina zai samo su?’
Ta yi bayanin cewa duk da mutanen yankin na kokarin hada kungiyoyin sa-kai domin kare al’ummarsu suna bukatar taimakon jami’an tsaro.