‘Yan uwa Musulmi mabiya darikar Shi’a kuma almajiran Malam Ibirahim El-Zakzaki sun gudanar da taron Mauludi na biyu na wannan shekarar ta bana a birnin Legas.
Taron Maulidin wanda ya gudana a bakin Masallacin Daramola Mark Jakshon da ke kan titin Champion Senima bakin Mile 12 International market, ya samu halartar wadansu manya-manyan Malamai mabiyan addinin shi’a almajiran Malam Ibirahim El zakzaki da suka fito daga Arewacin Nijeriya da sha’irai, cikinsu har da sha’irin Shi’ar nan Nura shahidi da sauran ‘yan uwa Musulmi mabiya tafarkin shi’a baki daya. manyan baki a wurin taron Mauludin sun hada da Malam Adamu, tsohon wakilin ‘yan uwa Musulmi na garin Jos, da Malam Usman yabo daga sokoto, wakilin ‘yan uwa na jihar Legas da sauran makamantansu.
Taron Mauludin da ya gudana a ranar Asabar din nan da ta gabata bayan bude taro da addu’a a ka umarci daya daga cikin manyan ‘yan kwamitin gudanarwa Alhaji Sunusi MarjiI, ya ce wani abu, inda ya fara da cewa, babu shakka ya yi farin ciki da zagayowar wannan rana da suke gudanar da Maulidin na wannan shekara ta bana, kuma ya yi wa manyan bakin fatan alheri da addu’ar komawa gidajensu lafiya.
Bayan Alhaji Sunusi marjiI ya kammala bayaninsa ne, aka sake ummurtar Babban bako kuma daya daga cikin manyan Malaman Shi’a da suka ziyarci taron Maulidin, inda shi ma ya cigaba da cewa lallai yana mai nuna farin cikinsa a game da zagayowar wannan shekara ta bana da suke gudanar da taron Mauludin wan nan shekara, sannan kuma ya umarci yan uwa musulmi mabiya Shi’a na Jihar Legas da Nijeriya baki daya da su cigaba da zaman lafiya da sauran Musulmi mabiya dariku daban-daban na kasar nan domin kasar ta Nijeriya ta cigaba da samun zaman lafiya.