Labarun yadda ake cin zarafin yara masu aikatau a sassan Nijeriya na da tayar da hankula. Yara kan yi aiki ne ba dare ba rana yayin da masu gidansu ke musguna musu. Ana biyan su abin da bai taka kara ya karya ba a wasu wuraren ma ba a biyansu ko kwabo. Ba wai yaki ne ya ci rayukan iyayensu ba, amma iyayen nasu ne suka mika su ga masu safarar su zuwa wajen aikatau din saboda tsanannin matsalar tattalin arzkin da suke ciki.
Dan abincin da aka rage suke samu su ci, shi ne kuma kadai abin da ke kwantar musu da hankali.
- NAF Ta Lalata Haramtattun Wuraren Tace Mai Guda 6 A RibasÂ
- Boss Mustapha Ya Karyata Zargin Satar Dala Miliyan 6.3 Daga CBN
Binciken da jaridar LEADERSHIP Hausa ta yi, ya nuna cewa, daukar yara aikin aikatau yana matukar karuwa a ‘yan shekarun nan a sassan Nijeriya.
Labaran halin da yara masu aikatau ke ciki yana tayar da hakula, yana kara nuna irin muguntan da ake nuna wa yara ‘yan aiki a gidajen da suke zaman aikatau.
Labarin Bolutife, ‘yar shekara 13, ta uku ga wasu iyalai matalauta a garin Akure ta Jihar Ondo, lamarinta tamkar iyayenta sun mika ta zuwa rayuwar bauta ne da kansu. A ranar da abin ya faru, wata rana ce a watan Yuni na shekarar 2022, ta ga mahaifinta mai suna Olumide, dan shekara 54, yana tattauanwa da wasu baki daga Abuja a cikin falon gidansu. Daga baya ta fahinci cewa sune wadanda za su dauke ta aiki sune kuma za su ci gaba da cin zarafinta. Bolutife ta zama ‘yar aiki kuma baiwa haka kuma wanda ya dauke aiki ya zama da ita tamkar matarsa yana lalata da ita a kan dan abin da bai taka kara ya karya ba da yake ba iyayenta.
A halin yanzu tana nan ta fara farfadowa bayan da ta yi wata 8 ana musguna mata. Ta samu ‘yanci ne bayan da wata kungiya mai zaman kanta ta ceto ta.
Amma ba duka suke samun irin wannan sa’ar ba, misali, labarin Jemilah ya fara ne a ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 2016 a garin Legas inda mutumin da ta ke yi wa aiki cikin fushi saboda bata wake buta yadda yake so ba ya ji mata ciwon da ya kai ga makancewarta a ido daya har a abada. Abin takaicin shi ne yarinyar ‘yar shekara 12 ta yi kokarinta na ganin ta ganmsar da uban dakin nata amma shi bai gani ba.
A wani lamari kuma da ya faru a garin Ikorodu ta Jihar Legas a ranar 19 ga watan Disamba 2016, wata mata mai yara uku wadda ya kamata ta zama mai kare rayuwa tare da shiryar da yara kamar yadda take yi wa yaranta amma sai ta zama sanadiyyar mutuwar ‘yar aikinta mai suna Faith, ‘yar shekara 10. Wannan lamarin ya tayar da hakulan al’umma kwarai da gaske.
Haka kuma a ranar 20 ga watan Mayu 2017. Wata ‘yar kasuwa ta yi wa ‘yar aikinta dukan kawo wuka inda dukan ya yi sanadiyyar mutuwarta, matar wadda ke daukje da ciki ta yi kokarin batar da gawar yarinyar amma asirinta ya tonu, daga nan doka ta yi halinta a kanta
Bincike ya kuma nuna yadda a watan Maris na shekarar 2018, aka samu irin wannan lamarin a birnin Legas, inda wata ‘yar aiki mai shgkara 10 a duniya ta kusan shekawa barzahu, laifinta kwai shi ne ta yi kokarin fada da yaran wadanda suka dauke ta aiki. Amma hukuncin da aka yi mata ya fi ainihin laifin da ta yi don kuwa an yi amfani da dutsen guga ne mai zafi ana dosanata mata a jiki, inda ya haifar da tabo masu yawa a jikinta.
An kuma samu irin wannan labarin a ranar 23 ga watan Afrilu na shekakar 2018, a Jihar Anambara, inda wata mai suna Uche Ugochukwu ta fito da maitarta da kuma tsananin muguntanta a kan ‘yar aikinta mai shekara 12, ta yi mata dukan kawo wuka abin da ya yi sanadiyyar ji mata ciwo a cikinta ya haifar mata da ciwon da za ta gama rayuwarta da su don ya shafi mahaifarta da wasu sassan hanjinta gaba daya.
Kididdiga daga Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO), ya nuna cewa, yara fiye da Miliyan 15 ke aikin aikatau a Nijeriya. Aikatau na yara na nufin duk wani aiki da za a iya sa yara da zai hana su cin gajiyar yarintarsu, wanda kuma zai iya hana su halartar makaranta a lokacin da ya dace wanda kuma zai iya cutar da su ta kowacce hanya, kamar yadda kundin Wikipedia na shekarar 2022 ya zayyana.