• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ministan Yaɗa Labarai Ya Karɓi Baƙuncin ‘Yan Jaridar Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

by Sulaiman
1 year ago
Jarida

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi maraba da sakin wasu ‘yan jarida biyu da aka sace daga gidajensu da ke bayan garin Kaduna a ƙarshen makon jiya.

Da yake jawabi a lokacin da ya karɓi baƙuncin ‘yan jaridun biyu, wato AbdulGafar Alabelewe na jaridar The Nation da AbdulRaheem Aodu na jaridar Blueprint, daga mai bai wa shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ministan ya yaba wa hukumomin tsaro bisa gaggawar ceto waɗanda lamarin ya shafa.

  • An Nada Ibrahim Rilwan A Matsayin Sabon Garkuwan Matasan Arewa
  • Matar Dan Jaridar Da ‘Yansanda Suka Kashe A Kenya Ta Samu Diyyar Dala 78,000

An saki ‘yan jaridar biyu tare da matar Mista Alabelewe da ‘ya’yan sa biyu.

Idris ya jajanta wa iyalan biyu, inda ya ce, “Muna matuƙar godiya da abin da kuka yi. Muna sane da cewa wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da kuke yi na ganin an kuɓutar da duk waɗanda aka sace tare da sake haɗa su da iyalansu.

“Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yin imani da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hukumomin tsaro.”

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Ya ƙara da cewa, “Hukumomin tsaron, a ƙarƙashin inuwar NSA, suna aiki tuƙuru domin ganin an kuɓutar da duk waɗanda aka sace ba tare da biyan kuɗin fansa ba.”

Da yake magana tun da farko, Malam Ribadu ya ce, an ceto mutanen biyar da aka sace ne sakamakon haɗin gwiwar da hukumomin tsaron suka yi wanda ya kai ga gudanar da bincike da ceto cikin gaggawa.

Da yake mayar da martani, ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, Mista Alabelewe, ya gode wa Ribadu da tawagarsa bisa gaggawar da suka yi.

Ya ce, “Aikin ceton da ya fitar da mu daga cikin daji a jiya ya ba mu fata a ƙasarmu kuma ya ba mu ƙwarin gwiwar yarda da cewa, gwamnati da gaske take wajen ganin ta magance wannan matsalar ta garkuwa da mutane.

“Ban taɓa tunanin cewa nan da mako guda da sace mu za mu kuɓuta ba. Muna godiya da gwamnati ta ɗauki mataki kuma ta tabbatar an sake mu.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Next Post
Wasan Karta Na Joe Biden Game Da Xizang Ya Gaza Tun Kan Ya Fara

Wasan Karta Na Joe Biden Game Da Xizang Ya Gaza Tun Kan Ya Fara

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.